Oshiomhole dan jagaliya ne, bai cancanci shugabancin APC ba – Gwamna Akeredolu

0

Gwamnan Jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya yi magana dangane da zargin da ake yi cewa shi da wasu gwamnoni na kulle-kullen tsige Shugaban Jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole.

Duk da cewa ya karyata zargin da ake yi masa, hakan bai hana shi cewa Oshiomhole dan jagaliya ba ne, wanda ya jagwalgwala jam’iyyar APC a cikin dan kankanin lokaci a yayin zabukan fidda-gwani na jam’iyyar da aka gudanar farkon watan Oktoba.

A cikin wata takardar da Babban Mai Bada Shawara kan Ayyuka na Musamman, Doyin Odebowale ya fitar ga manema labarai, Akeredolu ya bayyana cewa Oshiomhole tantirin dan jagaliya ne, wanda ya jagwalgwala jam’iyyar APC.

Ya ce Oshiomhole ya damalmala zabukan fidda gwani da APC ta gudanar a kasa baki daya, ta yadda zaben ya zama shirme, karfa-karfa, dauki-dora, dabanci da fashi.

Gwamnoni da yawa sun yi korafi dangane da yadda Kwamitin Gudanarwa na Kasa na APC ya baddala sunayen ‘yan takara da yawa wadanda ya mika wa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC).

Sun kuma yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya gaggauta sa baki a gyara shirmen da Oshiomhole ya yi.

Akeredolu, wanda shi ma duk yawancin ‘yan takarar sa ba su samu nasarar tikitin shiga zabe ba, ya ce wanda duk aka yi wa rashin adalci ya na da ‘yancin da zai fito ya nemi hakkin sa, kuma ya na da hakkin neman a tsige Oshiomhole.

Gwamna Akeredolu ya ce bai taba shirya wani zaman neman a cire Oshiomhole daga shugabancin jam’iyya ba.

Amma hakan ba zai hana ya nemi a tsige shi din ba, domin bai iya shugabanci ba, bai kuma cancanta ya zama shugaban jam’iyya ba.

“Shugabannin jam’iyya da suka karbi tulin makudan kudade daga hannun ‘yan takara barkatai, a lokacin shirmen da suka kira zaben fidda gwani, suka baddala sunayen wadanda ba su so da na wadanda suke so, sai su fito su fada wa jama’a dalilin su na yin haka.”

A karshe ya ce ga shi nan yanzu sai fallasa asirin su Oshiomhole ake yi, ana fito da yadda suka tafka rashin gaskiya kuru-kuru.

Share.

game da Author