Alamomi daga hukuncin da Kotun Koli ta yanke na nuni da cewa zai yi wuya APC ta shiga takarar Zaben Gwamna, na Majalisar Dattawa, Majalisar Tarayya har da na Majalisar Dokokin Jihar Ribas da ke karatowa a 2019.
Hukuncin da Kotun Koli ta yanke na soke zaben shugabannin jam’iyyar APC na jihar Ribas dungurugum, ya nuna cewa sauran ragowar karar da ke gaban Kotun Daukaka Kara ma dangane da zaben fidda gwani, zai kasance haramtacce ne.
Mummunan rikici a cikin jam’iyyar APC ta jihar Ribas ya kara ruruwa ne sakamakon adawar da ke tsakanin Ministan Harkokin Sufuri, Rotimi Ameachi da kuma Sanata Magnus Abe daga jihar.
Abe ya nemi tsayawa takarar gwamna, amma da ya ke jam’iyyar na a karkashin Ameachi, sai ministan ya kawo masa cikas din rashin amincewa.
TSAKANIN BIRI DA KAREN BAMAGUJE
Tun da farko matakin da Ameachi ya fara dauka, shi ne hana magoya bayan Abe shiga zaben shugabannin jam’iyya, da aka fi sani da ‘congress’. Ameachi ya kankane jam’iyya, sai abin da ya ga dama za a yi, kuma sai wanda ya ga dama zai ce a bi.
Shi kuwa Abe bai kwanta ya shantake ba, sai ya garzaya kotu, inda ya kalubalanci zaben shugabannin jam’iyya, a bisa dalilin cewa ba a bai wa magoya bayan sa damar shiga zaben ba.
A zaben shugabannin jam’iyyar dai an zabi dan gaban-goshin Amaechi, Ojukaye Amachree a matsayin shugaban jam’iyya na jiha.
Kwanki kadan kafin zaben sai Magnus Abe garzayawa Babbar Kotun a karkashin Mai Shari’a Chinwendu Nwogu, wanda shi kuma ya bayar da umarnin kada APC ta yi zaben shugabanni sai ta kammala hukuncin karar da Abe ya shigar.
Bangaren Ameachi ya daukaka kara, inda Kotun Daukaka Kara ta jingine hukuncin Babbar Kotu. Sai dai kuma Magnus Abe bai tsaya nan ba, ya garzaya Kotun Koli.
Kunnen-kashin da APC ta nuna na kin bin umarnin kotu har ta shirya zaben fidda-gwani a jihar Rivers a ranar 10 Ga Oktoba, hakan na nufin haramcin takarar dan gaban goshin Amaechi, Tonye Cole a matsayinndan takarar gwamna a jihar. A bisa dalilin cewa magoya bayan Magnus Abe nan ma ba su shiga zaben ba.
Haka kuma ya shafi zabukan fidda gwanin takarar sanatoci da na majalisar tarayya da na majalisar dokokin jihar.
Amma Kotun Daukaka Kara ba kai ga jaddada wannan hukuncin ba tukunna.
Abe ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa su Amaechi sun rika yin yadda suka ga dama, su ka ki bin umarnin kotu, suka gudanar da zaben shugabanninn jam’iyya da na fidda gwanin ‘yan takara, bayan kuma kotu ta ce kada a yi, tunda akwai shari’a da ake yi akan su.
A hukuncin da Kotun Koli ta yanke ranar Litinin da ta gabata, ta yi kaca-kaca da Kotun Daukaka Kara, a kan yadda ta soke umarnin da Babbar Kotu ta bayar.
“Wannan magana ce mai karfi sosai, kuma abin damuwa ganin yadda APC ta take dokar kotu, ta gudanar da abin da ta ga dama.” Haka Centus Nweze ya furta a madadin alkalan Kotun Koli biyar din da suka soke zaben shugabannin jam’iyyar APC na jihar Ribas.
RA’AYIN LAUYOYI A KAN HUKUNCIN DA AKA YI WA APC
Lauyoyi da dama da suka zanta da PREMIUMTIMES sun bayyana cewa hukuncin da Kotun Koli ta yi wa APC ya yi daidai, domin kiri-kiri ta take umarnin kotu.
“Bai ma kamata ba tun farko Kotun Daukaka Kara ta saurari karar da APC ta shigar a gaban ta ba, domin akwai umarnin dakatar da gudanar da zabe wanda ita APC din ta karya.” Inji lauya Malachy Ugwummadu, mazaunin Lagos.
Shi ma wani lauya mai suna Inibehe Effiong, cewa ya yi makomar wannan hukunci shi ne APC ba za ta iya tsaida ‘yan takarar gwamna, sanatoci, na majalisar tarayya da na majalisar dokoki ba a zaben 2019, a jihar Rivers.
Ya ce har sai an jira dayan hukuncin da wancan daukaka kara da ke gaban Kotun Daukaka Kara za ta yanke tukunna, wanda kuma zai iya haifar da daukaka kara zuwa Kotun Koli.
TAKARAR RIBAS: HANA WANI HANA KAI
Lauyan ya ci gaba da cewa a yanzu dai Magnus Abe na kwana da tashi a cikin murna, amma fa zai yi makukar wahala shi ma ya samu tikitin takarar ko da kuwa an soke Tonye Cole, dan takarar da Amaechi ya goya wa baya.
“Zai yi wahala, saboda Sashe na 87 na Dokar Zabe ya nuna cewa tilas sai an yi takarar fidda gwani dan takara zai iya fitowa. To tunda Kotun Koli da kan ta ta ce ba a yi zaben fidda gwani ba, kenan Abeh da Cole duk ba su shiga zaben fidda gwani ba kenan.” Inji shi.
Wani lauya mai suna Abdul Mohammed, cewa ya yi idan har Kotun Koli ba ta jingine hukuncin da Babbar Kotu ta yanke tun da farko ba, to babu yadda za a yi APC ta shiga zabuka a jihar Ribas.
Amma idan aka jingine hukuncin inji lauya Mahmood.
Ya ce amma idan aka jingine hukuncin, zai yiwu watakila APC ta fito da wasu ‘yan takara.
Sai dai kuma ya ce ganin yadda wuri ke kurewa, na wa’adin kwanakin da jam’iyya za ta iya sauya sunayen ‘yan takara, zai yi wahalar gaske APC ta tsaida ‘yan takara a jihar Ribas, muddin aka ci gaba da tafka shari’a.
MATSALAR AMAECHI A JIHAR RIBAS
Gwamnatin Jihar Ribas ta zargi tsohon gwamna Rotimi Amachi da salwantar da naira bilyan 112 wadanda ta ce ya tara bayan ya saida wasu kadarorin jihar a wani hamshakin attajiri, ana kusa ga yin zaben shugaban kasa na 2015.
Gwamanti karkashin sabon gwamna, Nyesom Wike na PDP sai ta nada kwamitin bincike, inda kwamitinn ya gano cewa dukkan kudaden da aka biya na kadarorin da Amaechi ya saida wa attajiri Tonye Cole, duk an karkatar da su.
Kwamitin bincike ya kuma zargi Amacchi da yin amfani da kudaden masu dama wajen daukar nauyin kamfen din Shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2015.
Nyeson Wike gwamna mai ci a yanzu ya zargi Amaechi da cewa ya na tsoron a tuhume shi, shi ya sa ya rika garzayawa kotu, ya na nema kotu ta hana binkiken sa da gwamnatin Jihar River ta nemi a ji tun cikin 2015 da ya kammala wa’adin san a gwamna, wanda daga bisani ya zama ministan Buhari.
An yi zargin cewa Amaechi na ta kokarin ya boye gagarimar satar da ya yine a jihar Ribas shi ya sa ya tsaida attajiri Tonye Cole, wanda ya saida wa kadarorin a matsayin dan takarar gwamnan jihar Ribas a zaben 2019.
A yanzu dai batun tuhuma ko rashin tuhumar Amaechi na can makale a Kotun Koli, sama da shekara daya, ba a yanke hukunci ba.