Tsohuwar ministan harkokin mata ta yi wa ofishin APC karkaf, inda ta kwashe duka kayan aikin da ta siya wa ofishin a Jihar Taraba.
Ofishin dai ya zama kamar kufayi yanzu domin har da AC, tebura, Komfutoci, Fitillu, Labule, takardun aiki, ledan kasa, butoci, kofuna duk ta sa a kwashe su.
Idan ba a manta ba Mama Taraba, Aisha Alhassan, ta tattara nata-inata ta yi sallama da jam’iyyar APC tun bayan hana ta yin takara a inuwar jam’iyyar da APC tayi.
Hakan bai yi mata dadi ba inda nan take ta yi murabus daga kujerar minista da take rike da shi ta canja sheka zuwa jam’iyyar UDP.
Kakakin jam’iyyar na jihar Taraba ya bayyana cewa wannan abu da Aisha tayi shine karshen rashin mutunci da nuna karanta da ya taba gani.
Ya ce Aisha bata saka wa jam’iyyar da ta goya ta ba ta yi mata komai. Maimakon ta saka mata da Alkhairi sai ta saka mata da tsiya.
Sai dai kuma Aisha ta maida masa da martani, inda ta shaida masa cewa idan bai sani wannan kayayyaki da kudin ta ta saye su.
” Wadannan kayayyaki da kudina na siya. Gumi nane ba na APC ba saboda haka tunda abin rashin mutunci ne nima ba zan iya hakuri ba dole ne in gurza musu suji.
” Magoya baya na ne suka bukaci ayi haka kuma da gaskiyan su domin yanzu bana jam’iyyar APC kuma banga dalilin ci gaba da abri musu wahala ta ba. Tuni yaran suka far wa ofishin suka cire komai da na siya.