KISAN JANAR ALKALI: Sojoji sun gabatar da mutane 13 da ke cikin wadanda ake zargi

0

Hukumar Tsaro ta Sojojin Najeriya ta gabatar wa manema labarai da wasu mutane 13 da ake zargin na da hannu wajen bacewar Janar Idris Alkali Mai Ritaya, a Jos.

An gabatar da wadanda ake zargin ne a yau Laraba ga manema labarai a Jos, babban birnin Jihar Filato inda a can ne dama ake zargin an kashe shi.

Janar Alkali ya bata ne tun a ranar 13 Ga Satumba, 2018, bayan da ya bar Abuja da safiyar wannan rana da nufin zuwa Bauchi.

Kwamandan Rundunar Garison ta 3 da ke Rukuba, Jos, Umar Muhammad, ya ce za a gabatar da wadanda ake zargin ga ‘yan sanda domin yi musu cikakken bincike kuma a gurfanar da su a yi musu hukunci.

Ya ce an kama wadanda ake zargin ne a yankin da ke kusa da tafkin da aka tsamo motar Janar Alkali a ciki.

Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Najeriya Tukur Buratai ne ya kafa kwamitin gano duk inda Janar Alkali ya ke, kuma suka shiga bincike.

Hukumar sojojin sun ce bayan sun tsananta bincike, sai suka takaita binciken na su kacokan iyakar wani katon kududdufi da ke kauyen Dura-Du, cikin Karamar Hukumar Jos ta Kudu.

Bayan da aka shafe makonni biyu ana zuke ruwan da katon bututu, sai aka tsinci motar Janar Alkali a cikin tafkin da kuma wasu motoci biyu.

Muhammad ya ce sojoji sun mamaye mutanen kauyen inda suka yi nasarar kama wasu da ake zargi.
An kama su an kai su barikin soja kuma an dauki bayanan su tare da tantance kowanen su dangane da masaniyar da ya ke da ita kan bacewar Janar Alkali.

“Wadanda za a damka wa ‘yan sanda din sun hada har da wadanda aka kama su da muggan makamai tare da su ba tare da mallakar lasisi ba.

“Akwai kuma wadanda suka ji kuma suka ga mugayen da suka tura motar Janar Alkali a cikin kududdufi, amma ba su kai rahoto ga jami’an tsaro ba.”

Ya ci gaba da cewa wadanda ke da ainihin hannu wajen kama Janar Alkali da kuma tura motar ta sa a cikin tafki duk sun tsere, amma kuma duk sojoji sun san su.

Sai ya ce ana ta kokarin ganin duk ma inda suka shige an kamo su, domin akwai hotunan su a hannun jami’an tsaro a wurare da dama.

A karshe ya roki mazauna yankin da suka arce tun bayan da aka fara binciken cewa kowa ya dawo gidan sa, ba za a taba lafiyar su ba.

Share.

game da Author