Akalla an kashe mutane biyar a Karamar Hukumar Ebonyi ta jihar Ebonyi, tsakanin al’umma Mgbo da kuma al’ummar Agila na jihar Benuwai.
Mazauna yankin sun yi ikirarin cewa jama’ar Agila ne suka shiga kauyukan su guda biyu suka kai musu farmaki.
Sama da shekaru 30 wadannan al’umma da ke makautaka da juna ke cikin rikici wanda ya yi sanadiyyar rasa rayukan jama’a da dama.
Gwamnan Ebonyi, David Umahi ya nuna matukar damuwar sa dangane da kisan da aka yi wa mazauna yankin na Mgbo.
Shi ma Mataimakin Gwamna, Kelechi Igwe da ya kai ziyara a yankin, a a madadin gwamnan, ya ziyarci iyalan wadanda aka kashe din ya yi musu ta’aziyya a kauyukan Ekwashi da Ukwagba.
Duk da cewa al’ummar yankin sun sha fama da hare-hare daga al’ummar Agila daga jihar Benuwai, Mataimakin Gwamnan ya yi kira da a zauna lafiya, domin hukuma za ta dauki mataki.