2019: Jam’iyyar ADC ta tsaida mace takarar gwamnan Filato

0

Jam’iyyar ADC ta zabi Margret Inusa a matsayin ‘yar takarar gwamnan jihar Filato a zaben gwamna da za a gudanar cikin Fabrairu, 2019.

An zabi Fasto Margret ce tare da wasu ‘yan takarar mukaman siyasa daban-daban a jihar a zaben da jam’iyyar ta yi na fidda-gwani ranar Lahadi da ta gabata.

Baya ga ‘yar takarar gwamna da suka tsaida, jam’iyyar ta kuma fidda ‘yan takarar Majalisar Tarayya takwas da kuma na majalisar dokoki ta jiha su 24.

Mai kula da zaben Ibrahim Pam ne ya bayyana haka, bayan zaben da ya gudanar na wadanda za su wakilci jam’iyyar a zaben 2019.

Margret dai ‘yar kasuwa ce kuma fasto. Ta yi alkawarin idan ta ce za ta tabbatar da tsaro da inganta jihar Filato.

Za ta fafata da dan takarar APC, Simon Lalong da na PDP Jeremier Useni.

Share.

game da Author