Mai wa’azi kuma dan siyasa, Tunde Bakare, ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya gaggauta yin amfani da karfin ikon sa na shugaban kasa, ya kira taron gaggawa kan Makomar Kasa, domin a tattauna zaman sasantawa tsakanin juna, sake zaman dunkulewa wuri daya a cikin tsari na zaman amana da kuma sake fasalin kasar nan.
Bakare wanda a zaben 2011 shi ne ya fito ma matsayin mataimakin Muhammadu Buhari a karkashin CPC, ya bayyana haka kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa, NAN ya ruwaito, a Ikeja, a wani taron manema labarai.
Ya ce ya yi wannan kira ne ganin yadda manyan masu tofa albarkacin bakin su dangane da inda Najeriya ta dosa, ke ta kumajin cewa lokaci ya yi da za a kira taron makomar kasar nan.
Ya ce haka ne zai kara dankon hadin kai, tabbatar da zaman lafiya, ci gaba da kuma shimfida adalci a kan abububan da suka jibinci kason arzikin kasar nan.
Bakare ya kara da cewa Buhari ya tuntubi Majalisar Tarayya da ta Dattawa da kuma Majalisar Zartaswar kowace jiha, ta yadda zai kafa kwamiti na shugaban kasa da zai ja ragamar gudanar da taron makomar kasar.
A karshe ya ce Buhari ya yi kokari ya dora jan namijin da ba shi da ganin kyashi, mai kishi kasar nan, ba kishin bangaranci ba, kuma mai jaddada adalci wanda zai ja ragamar sake dinkewar kasar nan daram dam-dam, daga irin zaman doya-da-manjan da ake yi yanzu tsakanin wannan yanki da wancan.
Ya ce mai kishin da kudi ba za su iya rufe masa ido ba ne ya kamata a dora a kan wannan mukami.