” Na yarda da kayen da Atiku ya yi mana, kuma zan taya shi kamfen”- Jang

0

Daya daga cikin ‘yan takarar shugabancin kasar nan a karkashin jam’iyyar PDP, Jonah Jang, ya taya Atiku Abubakar murna a kan nasarar da ya samu a kan su. Sannnan kuma ya yi alkawin goya masa baya har ya samu nasara.

Jang ya yi wannan sanarwar taya murna da alkawarin goyon baya ne a cikin wata takarda da ya raba wa manema labarai, a Jos, Babban birnin jihar Filato.

“A farkon gabatowar zaben 2019, na gina kaina a kan yakinin fitowa takarar shugabancin kasa a zaben 2019. Amma daga yanzu wannan muradi nawa babu shi, domin nasarar da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya samu, ta tsaida nawa shirin.

“A madadi na da tawagar yakin neman zabe na, muna taya Atiku murnar wannan nasara da ya samu a zaben da a tarihi ba a taba yin irin sa a kasar nan ba.”

Jang, wanda ya zo na biyun na karshe da kuri’u 19, ya bayyana Atiku a matsayin shugaban da ke jira kawai a rantsar da shi.

Daga nan sai ya roke shi da cewa idan ya yi nasara to ya duba abubuwan da ke damun yankin Arewa ta Tsakiya.

Share.

game da Author