ZABEN FIDDA DAN TAKARA: Wane gwanin PDP zai iya cirar tuta?

0

‘Yan takarar shugabancin kasar nan a karkashin jam’iyyar PDP sai kara sa himma su ke yi wajen neman hadin kai da kuma goyon bayan wakilan jam’iyya masu yin zaben a ranar zaben fidda gwani da jam’iyyar za ta gudanar a cikin farkon watan Oktoba.

Alamomi na nuna cewa da wuya a iya cimma matsayar yin sulhun tsayar da dan takara daya tilo, ba tare da an je filin zaben fidda gwani ba.

Da ya ke an amince cewa dan takarar PDP daga Arewa zai fito, za a iya cewa duk wani wanda ya fito daga kudancin kasar nan, tamkar ihun-ka-banza ne ya ke yi a cikin dokar jeji inda ba shi da mai kawo masa agaji ko daya.

To ko a nan Arewa, daya daga cikin ‘yan takarar, wanda ya fito daga Arewa ta Tsakiya, wato Bukola Saraki, kwanan nan ya ce kamata ya yi dan takarar ya fito daga yankin su, a nan ya na nufin shi kenan.

Su ma sauran duk da sun ce duk wanda aka tsayar, to za su bi shi, wanan ba ya na nufin cewa sauran janyewa za su yi kai-tsaye salum-alum ba.

Hakan ya nuna zai iya faruwa a jiya bayan da Sule Lamido ya maida wa Atiku Abubakar raddin cewa ba zai iya janye masa takara ba.

Daga cikin ‘yan takarar jam’iyar PDP, Lamido ne wanda ya fi dadewa ya na takara, kuma shi ne wanda ya fi saura karade fadin kasar nan ya na neman goyon bayan jama’a.

Har iya yau Sule Lamido ne ya fi saura dadewa a cikin PDP, domin da shi aka kafa jam’iyyar, sannan kuma tun da ya shiga cikin ta bai taba ficewa ba ko a rana daya.

Lamido ya fi kowa tutiya da PDP da kuma jimirin jure caccakar adawa. A yanzu ya na fuskantar shari’a a kotu. Sai dai kuma wannan ba za a ce wani dalilin da zai rage masa karfi ba ne, domin akasarin jigagigan APC babu wanda ba ya fuskantar shari’a a kotu.

Sannan kuma manyan makusantan Shugaba Muhammadu Buhari su takwas da ke sahun gaban yi masa kamfen na sake tsayawa takara, duk sun a fuskantar shari’a kotu, sai kuma masu rikita-rikita a ofishin EFCC.

Aminu Waziri Tambuwal na da tasirin yin nasara, sai dai matsalar sa ita ce har yau bai fara bude ko da ofisoshin takarar sa a jihohi kamar irin yadda Sule Lamido ya yi ba.

Za a iya cewa Atiku da Tambuwal za su fuskanci matsaloli, musamman Atiku ya fi karkata wajen gina karfin magoya baya a kudancin kasar nan, a maimakon Arewa.

Wanda kuma ake ganin zai iya yin nasara shi ne Rabi’u Kwankwaso, wanda shi ma ya fice daga APC cikin watan Yuli, zuwa PDP.

Kwankwaso na da dimbin magoya baya, kuma ya jina mabiyan siyasar sa na akidar Kwankwasiyya a fadin Najeriya. Kamar yadda rasa Kwankwaso a PDP zai iya zame wa jam’iyyar babbar matsala, haka kuma samun nasarar sa a takarar shugabanci a zaben fidda gwani zai zame wa jam’iyyar alhari.

Sai dai me, Sule Lamido ma fa ba a yaba, domin ya gina jama’a, ya kafa magoya baya, ya bauta wa PDP, ya yi biyayya kuma kamar yadda ya fada da kan sa, ya fi sauran sanin siyasa. Kuma yayi aiki an gani a lokacin da ya na gwamnan Jigawa.

Sauran ‘yan takara irin su Datti Ahmed, Tanimu Turaki, kuwa ana ganin ko da lalama za a iya rokon su su janye, kuma su yi hakuri a tafi tare, domin a tsira tare.

Shi ko shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, na da matukar karfi a wannan kokawa da za ayi. Muddun ba janye wa yayi ba toh, za a ko iya cewa akwai sauran rina a kaba, domin shima kasaitaccen attajirine da zai iya ja da ko ma waye a jam’iyyar.

‘Yan takara kamar su tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ahmed Makarfi, Ibrahim Dankwambo, Jonah Jang da David Mark kuwa duk ana yin hasashen cewa sun jingina ne da jam’iyyar da inda karfin ikon jam’iyyar ya karkata. Kila akwai alkawura da aka yi a tsakanin juna.

Ana dai ganin babban abin da zai fi tasiri a zaben fidda gwanin jam’iyyar PDP shine wanda yafi samun goyon bayan gwamnonin jihohin PDP din, sannan kuma da wanda Jam’iyya ta karkata ga. Ana sa ran wanda yafi fallo naira shima zai yi tasiri.

Ko ma dai me kenan, za a tantance a ranar 5 Ga Oktoba mai zuwa.

Share.

game da Author