Ranar 9 Ga Satumba, 2018, rana ce da ‘yan jam’iyyar APC na jihar Zamfara ba su taba mantawa da ita ba. Rana ce da ta zo wa wasu manaya da kananan mabiya jam’iyyar APC na jihar da bazata. Rana ce da aka kusan wayar gari ana takoke da waswasin hukuncin da jam’iyyar APC ta yanke dangane da wadanda za su tsaya takarar mukamai daban-daban a jihar, kama daga na gwamna har zuwa na majalisar dattawa da na tarayya, har ma da na jihohi.
Zai yi kyau a yi yi dalla-dalla ko kuma filla-fillar yadda ta kasance, tare da yin tariyar abin da ake tunanin zai kasance kafin hakan ta kasance, sai kuma a bayyana shin me ya sa abin da ake tunanin shi zai kasance, amma ba shi din ne ya kasance ba:
Tun tuni an yi tunanin cewa Gwamna Abdul’aziz Yari zai yi irin abin da Ahmed Sani Yerima ya yi a lokacin da zai bar mulki, inda ya tsaida mataimakin sa Mamuda Shinkafi ya zama dan takara, kuma shi ya yi nasara.
A wancan zangon a jihar Zamfara ne kadai inda gwamna ya tsaida mataimakin sa ya gaji kujerar sa.
A tunanin jama’a shi ne a yanzu Gwamna Yari zai tsayar da mataimakin sa, mutumin da ya ke yi masa biyayya, wato Wakkala Muhammad a matsayin dan takarar jama’iyyar APC, tunda shi Yari zai kammala zangon sa na biyu kenan.
Kallo ya koma sama a siyasar Zamfara, inda Yari da jam’iyyar APC suka tsaida Muktar Shehu Idris a matsayin dan takarar gwamna na APC, maimakon Muhammad Wakkala.
Wakkala ya dade a cikin siyasa ko kuma a ce cikin mulkin jihar Zamfara. A lokacin mulkin Yerima a 1999, shi ne Darakta Janar na Hukumar Shari’a ta jihar. A takaice dai daga ofishin sa ne aka rika gudanar da harkokin shari’ar musuluncin Zamfara a wancan lokacin.

Baya ga wannan kuma, kafin Wakkala ya zama mataimakain gwamna, ya yi kwamishinan shari’a na jihar. Haka nan kuma a yanzu da rikicin mahara da masu satar shanu ya yi kamari a jihar Zamfara, Wakkala ne shugaban kwamitin tabbatar da tsaron jihar.
WANCAKALI DA WAKKALA
Idan har aka sake APC ta samu matsala a jihar Zamfara, to da dama na ganin cewa alhakin Wakkala ne zai kama jam’iyyar har ta yi asarar kujerar gwamna, ko kuma asarar wasu kujeru na jiha ko na tarayya. Domin jama’a da dama hakan bai yi musu dadi ba.
Matsawar PDP ta kara kaimi tare da tashi tsaye, to za ta iya bada mamaki a jihar.
YARI NA NEMAN YARFAR DA YERIMA
Sai kuma batun kokwar neman kujerar Sanata mai wakilta Zamfara ta Yamma, kujerar da a yanzu Sanata Yerima ke kai. Wannan kujera an bada takarar ta ga gwamna Abdul’aziz Yari.
Tambayar da mutane ke yi, ita ce, shin wai Yeriman ne da kan sa ya ce ya gaji da kujerar Sanata da ya ke a kai tun daga 2007 har zuwa yau, ko kuwa ta yi tsami ne tsakanin sa da yaron san a siyasa gwamna Yari, har suke neman nada damben takara a tsakanin su?
Yayin da wasu ke cewa ta yi tsami a tsakanin su, wasu kuma na cewa dama can shiri ne aka yi da kuma yarjejeniya cewa a shekarar 2019 Yerima zai hakura ya bar wa Yari shi ma ya hau, ya dandana domin ya ji irin bambancin da ke tsakanin kujerar gwamna da ta sanata.
Wasu kuma sun tafi a kan cewa, a’a, an kulla yarjejeniya ce amma daga cikin sharuddan su ne za a yi wa Yerima tukuicin wasu kujeru. Kujerun da magulmata ke cewa an bai wa Yerima Tukuicin kuwa sun hada da ta dan majalisar tarayya da aka ce ana bai wa surikin sa, sai kuma wata ta dan majalisar jiha da aka ce an bai wa dan sa.
Ko ta ya za a fassara abin dai, daga inda aka ce yaron ubangida ya zama gwamna, to ya fa zama abin da Hausawa ke cewa, “Na kawo karfi, ya fi wane ya grime ni.”
Ko ma dai ya abin ya ke, za a iya cewa mataimakin gwamna Wakkala ne aka yi wa wa-ka-ci-ka-tashi. Koda ya ke labari ya bazu cewa shi ma ya sayi fam na takarar gwamna, duk kuwa da cewa tuni APC a jihar ta wakkala wakilcin kujerar gwamna din ga wani daban, ba Wakkala Muhammad ba.
Idan haka ne kuwa, ashe ta mawaki Dangiwa Zuru kenan, da ya ke cewa: “Ashe hwada bai kare ba, rincimi bai bai kare ba, kokawa ba ta kare ba.” Ga dai Yerima daure da warki, Yari zai daura na sa warkin kamar yadda shi ma Wakkala ya rike na sa warkin a hannu, sauran sa kawai ya daura a fara kokawa.
Su kuwa Zamfarawa da su yi zabe sun kwana da sanin wani baiti na Musa Dankwairo da ya ke cewa: “Da burgu da zomo da kurege, kowane na shi hali ya kai bamban…..”
To bari mu gani wa za a bambance a ranar tantancewa ne?