2019: KAR TA SAN KAR A KANO: Kwankwaso, Takai da Ganduje, Shekarau

0

Yanzu dai ta tabbata sarka da igiyar siyasar jihar Kano ta rikirkice, domin manyan abokan hamayya hudu sun sa kafar wando daya, kowa na rike da tazugen wando, har sai zaben 2019 ne zai tabbatar da wanda zai iya yin galaba kan wandon, har ya sabule kafafuwan saura.

Hadewar da aka yi tsakanin Sanata Rabi’u Kwankwaso da dan takarar gwamnan jihar Kano karkashin jam’iyyar PDP, Salihu Sagir Takai, ta ba kowa mamaki. Domin Takai ya fusata ne tun cikin 2014 ya fice daga APC tare da ubangidan sa, Malam Ibrahim Shekarau, tun bayan da Gwamnan lokacin Rabi’u Kwankwaso ya koma APC daga PDP, kuma uwar jam’iyya ta ba shi ragamar rikon jam’iyyar a Kano.

Ana mamakin yadda Takai ya ki bin Shekarau zuwa komawa APC jam’iyyar su ta asali, inda suka fito da farko. Sai dai kuma da yawa na ganin cewa hadewar Kwankwaso da Takai za ta yi tasiri sosai, domin Shekarau shi kadai ya koma cikin APC sai kuma tsirarun magoya bayan sa wadanda ake kira da suna ‘PDP Islamiyya.’

Da yawan ‘yan PDP ba su bi Shekarau sun koma APC ba, dama kuma PDP na da magoya baya daga bangarori daban-daban.

Dalili kenan ake ganin idan aka sake goguwar ballewa daga Ganduje ta dan sake kadawa, to Takai zai iya kada Ganduje a ranar zaben gwamna.

A na sa bangaren, Ganduje zai iya yin tutiya da cewa ya samu Ibrahim Shekarau, ba don komai ba sai saboda Kwankwaso da dimbin mabiyan sa sun yi wa APC mummunar gibi.

Saboda haka shigowa ko kuma komawar Shekarau cikin APC, jam’iyyar sa ta da, karin karfi ne ga Gwamna Ganduje ko da kuwa magoya bayan Shekarau ba su da yawa.

Ba kamar Shekarau ba, Kwankwaso kusan tare da ilahirin magoya bayan say a koma PDP, shi ma jam’iyyar sa ta ainihi. Sannan kuma ba a samu wasu manyan jiga-jigan sa sun yi masa tawaye ba.

Raba hanyar Kwankwaso da Ganduje zai iya zama alheri ga Shekarau, domin zai daina zaman-dirshan a gida, duk kuwa a baya ya nemi tsayawa takarar shugabancin kasa a karkashin PDP, kafin ya fice daga jam’iyyar.

Dama ana ganin neman takarar Shekarau, ida sunnah ne dai kawai, wai makaho da waiwaye, inji Hausawa. To ganin cewa ya yanki fom na neman takarar Sanatan Kano ta Tsakiya, a karkashin APC, kuma zai gwada kwanji ne da Sanata Kwankwaso mai rike da kujerar.

Dole Kwankwaso ya nemi kare kujerar sa, idan har PDP ba ta tsaida shi takarar shugabancin kasar nan ba.

Kamar yadda kare kujerar Kwankwaso ta Sanata za ta yi masa wahala yadda wasu ke hasashe, haka shi ma Ganduje ba lallai ba ne ya iya kare kujerar sa ta gwamnan jihar Kano, ganin yadda ake kallon siyasar Kano, harkar tuggu ne irin na ‘yan garin nan, sai kuma wanda ya san garin nan.

Share.

game da Author