KURUNKUS: Zaben Osun bai kammalu ba, za a sake zabe a inda aka soke zabuka – Hukumar INEC

0

Hukumar zabe ta Kasa ta sanar cewa zaben jihar Osun da aka yi bai kammalu ba domin kuwa sai an sake zabe a mazabun da aka soke zabe.

Joseph Fuwape ne ya fadi haka a karshen bayyana sakamakon zaben gwamnan jihar da aka yi.

Fawupe ya ce dalilin da ya sa babu wanda ya sami nasara a zaben shine ganin cewa kuri’un da dan takarar jam’iyyar PDP ya doke takwaran sa na APC da shi bai kai yawan kuri’un da aka soke ba a zaben.

Dan takarar PDP Isiaka Adeleke ne ya lashe zaben da yawan Kuri’u sai dai ya doke takwaran sa na jam’iyyar APC da yawan Kuri’u 354 wadda hakan bai kai yawan kuri’u sama da 3000 da aka soke ba.

A ci gaba da bayani da yayi, Fawupe ya kara da cewa sai dai kuma ganin cewa wadannan Kuri’u bai kai yawan kuri’un da aka soke a mazabu da dama a jihar ba da suka kai akalla 3498 ya zama dole a sake zabe a wadannan yankuna kafin nan a sami sahihin sakamakon zabe da zai tabbatar da wanda ya ci zaben.

Wannan zabe dai ya tada wa ‘yan jam’iyyar APC hankali matuka ganin cewa duk da suna ke mulki a jihar wankin hula dai ya kai su dare.

Osun Results

Osun Results

Share.

game da Author