Jim kadan bayan da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta bayyana cewa zaben gwamnan jihar jihar Osun da aka gudanar jiya Asabar, bai kammalu ba, PREMIUM TIMES HAUSA ta kutsa kai cikin taskar adana bayanan INEC domin yi wa wannan kiki-kaka filla filla.
INEC dai ta ce zaben na jihar Osun bai kammalu ba, saboda ratar kuri’un da wanda ya yi nasara (PDP) da kuma wadda ta yi ta biyu, (APC), ba su kai yawan kuri’un da aka soke ba. Don haka dama a rubuce ya ke a dokar INEC cewa idan hakan ta faru, to za a sake zabe a wasu rumfunan da aka yi tankiyar kuri’un da aka soke.
ZABEN OSUN: ASALIN TIRKA-TIRKAR
An gudanar za zaben gwamna ranar Asabar, inda sakamakon zabe ya nuna cewa ‘yan takara biyu da ke kan gaba –Sanata Ademola Adeleke na PDP., ya samu kuri’a 254, 698. Shi kuma Gboyega Oyetola na APC ya na da 254, 345.
*Ratar da ke tsakanin su ta kuri’u 354 ce kacal, wadanda a doka ba su kai yawan kuri’un da aka soke ba, har guda 3498.
*Dokar Zabe ta Sashe na 153 ya jaddada cewa matukar ratar yawan kuri’un wanda ya zo na daya shi da wanda ya zo na biyu ba ta kai yawan kuri’un da aka soke ba, to zabe bai kammalu ba, har sai an sake yin zaben raba-gardama a yankunan da aka soke kuri’un.
MATAKAN RASHIN KAMMALUWAR ZABE
Cikin wata doguwar makala da Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu ya taba gabatarwa, bayan hawan sa shugabancin INEC, ya ce:
INDA HARGITSI YA HANA A YI ZABE
“A zabukan da suka gabata can baya, ’yan siyasa kan hargitsa zabe a inda suke ganin ba su da karfin samun kuri’u, ta haka sai su yi nasara a yankin da suka fi karfi. A kan haka ne a yanzu sai INEC ta ce idan aka hargitsa zabe a ko’ina, to INEC za ta sake bai wa jama’ar wannan yanki damar sake jefa kuri’a. Saboda kuri’a ce a kasar nan ke zabar mutum, don haka tilas ita ce za ta yi aiki kenan.
“An aiwatar da irin wannan tsari ba sau daya ba a zaben 2011, idan za ku iya tunawa, ko zaben jihar Imo ai bai kammalu ba, sai da INEC ta kammala zabe daga bisani. Haka ma a waccan shekarar a zaben gwamnan Bauchi sai da INEC ta sake zabe a kananan hukumomi biyu a jihar Bauchi, wato Ningi da Misau. Haka yake a zaben jihar Anambra a zaben gwamna cikin 2013, zabe bai kammalu a kananan hukumomi 16 ba, sai da INEC ta koma ta kammala su daga baya.
“Haka kuma aka yi a jihohin Taraba, Abia da Imo da zaben 2015, duk sai da INEC ta sake zabuka a wasu yankunan da zabe bai kammalu a wadannan jihohin ba a 2015.
INDA ZABE BAI KAMMALU BA TUN A MAZABU
“Sannan kuma akwai inda ake samun zabe bai kammalu ba tun ma a mazabu. Gaba dayan dalilin bayyana hakan shi ne domin a bai wa jama’a damar jefa kuri’ar su. Domin kuri’a ce abin amfani ko dogaro a wajen zaben shugabannni. To idan an fahimci abin da duk na bayyana, sai kuma mu dawo, shin me ya sa ake samun zabukan da ba su kammalu ba?
*“Na farko dai akwai sabon sauyin canji a zabukan 2015, musamman sakamakon shigo da na’urorin zamani wajen zabe. Amma dai duk da hakan, ba mu kai ga matakin da ake son a cimma ba. A karon farko a zaben 2015 an samu karancin ratar kuri’u tsakanin jam’iyyar da ta yi nasara da kuma wadda aka kayar. Kuri’a milyan 2.5 ce mafi karancin yawan ratar kuri’u a zabukan shugaban kasa tun daga 1999.
*“Na biyu kuma a da an saba ganin jam’iyyar da ta yi nasara na tserewa fintinkau da rata mai yawa sakamakon karfinta da kuma karancin karfin tarkacen kananan jam’iyyun adawa. Amma a yanzu kuwa akwai manyan jam’iyyu biyu masu karfi.
*“Na uku kuma, akan samu takara ta yi zafi sosai. Misali mu dauki jihar Kogi inda gwamna da ke kan mulki ya kafsa da tsohon gwamna. Kun ga an samu gaggan ‘yan takara biyu da suka fito daga manyan jam’iyyu biyu kenan. Haka nan a Bayelsa gwamna mai rike da kujera ne ya kara da tsohon gwamna. Kusan hakan za a ce a Ribas yayin sake zabe. Kun ga kenan akan samu inda manyan jam’iyyu biyu sun fito da gaggan ‘yan takara biyu.
*Wani dalilin kuma shi ne, yadda a yanzu zabe na kara samun inganci, inda a yanzu kuri’a ce ke tabbatar da sakamakon zabe. Duk inda ka duba sakamakon kowane bangare, za ka ga cewa ratar ba ta da yawa soasi. Ka dauki zaben jihar Bayelsa, inda gwamnan da ya tsaya kuma ya sake nasara a zaben 2015. Ka duba can baya a zaben 2011, ai da kuri’u 417,500 ya bai wa na biyu rata. Amma a zaben 2016 a watan Janairu, da kuri’u 50,000 kacal ya yi rata. Wannan kuwa na nuna maka yadda takarar ke kara zafi sosai kenan.
Zabe dai na kara samun inganci idan muka yi la’akari da jihar Kogi. Ratar wanda ya yi nasara da wanda aka kayar ba ta da yawa, ba ta kai yawan ratar kuri’un da aka soke ba na inda zabe bai yiwu ba. To INEC dama ta bayar da damar cewa duk inda zabe bai yiwu ba, za a sake bai wa masu jefa kuri’a damar zaben wanda ran su ke so ya shugance su.
*“Wato da wani muke goyon baya, ai da mun bayyana sakamakon zaben, amma sai ba mu yi haka din ba. INEC ba ta azarbabin bayyana sakamakon zabe ko ta halin kaka. Tilas a bai wa ‘yan Najeriya damar zaben wadanda suke so su shugabance su, kuma mun dade muna neman wannan damar. Ni ban damu da sukar da za a yi mana ba, matsawar dai mun aiwatar da nauyin da aka dora mana a kan gaskiya.
*“Wato dai kowane zabe kan zo da irin nasa kalubalen. Idan akwai mutum daya a kasar nan da zai fi kowa son a ce kowane zabe ya kammalu a kan lokaci, to shi ne shugaban Hukumar Zabe, domin duk abin da ya faru ni ne zan sha suka da caccaka.
*“Babban misali shi ne zaben da aka yi a FCT Abuja. Sannan kuma duk inda ba a yi wani tashin hankali ba za ka ga an kammala zabe cikin natsuwa, saboda za ka ga babu yawan kuri’un da aka soke, kuma babu yawan ratar kuri’u tsakanin wanda ya yi nasara da wanda aka kayar. A duk inda aka yi tarzoma ko rikici kuwa za ka ga rikicin ya shafi sakamakon zaben, saboda a yanzu zaben ya kara inganta, kuma takara na kara zafafa.
*“Kwanan nan a cikin 2016 din nan, mun gudanar da zaben cike gurbi a jihar Yobe. Daga cikin mazabun da aka gudanar da zabuka har da Tarrmuwa da ta kunshi kauyen Shekau. Babu wani tashin hankali a kauyen Shekau. Haka mun gudanar da zabe a Karamar Hukumar Gulani wacce ba ta dade daga cetowa a hannun Boko Haram ba. Abin sha’awa shi ne tun wajen karfe daya na rana aka bayyana wanda ya yi nasara. Saboda babu wani rikici kwata-kwata. Amma fa a inda aka yi rikici ko a ina ne, to babu yadda za a yi a ce zabe ya kammalu.Wannan haka yake a cikin tsarin ka’idojinmu na zabe.” A cikin makalar Shugaba INEC, 2016.
RABE-RABEN RASHIN KAMMALUWAR ZABE
Rabe-raben Rashin Kammaluwar Zabe, sun kasu gida uku, wadanda a Turance ake kira (i) Run-off Election); (ii) Re-run Election; (iii) Inconclusive Election.
Dukkan wadannan rabe-raben zabukan da ba su kammalu ba, ma’anar su dai daya ce, wato ba za a iya bayyana sakamakon zabe ba, har sai an sake zabuka a wasu mazabu, yankuna ko kananan hukumomi inda daya daga cikin wadancan sabubba uku na Turanci suka faru.
Sai dai kuma duk da cewa ma’anar ta su daya ce, wato sake yin zaben-raba-gardama a wasu mazabu ko rumfuna, wannan ma’anar ta yi rassa har guda uku, kamar yadda za a fayyace wa masu karatu dalla-dalla.
*Run-off Election: Wannan zaben-raba-gardama ne, wanda ake sake yi idan dan takarar gwamna ko na shugaban kasa ya kasa yi wa wanda ya zo na biyu ratar da ta wajaba a ce ya yi masa a fadin jihar, ko kuma kasa.
*Re-run Election: Shi kuma wannan zabe ne wanda ake sakewa yayin bayan wanda aka gudanar da farko ya hadu da magudi ko kuma an samu inda aka ki bin sharuddan da INEC ta gindaya a bi wurin yin zabe.
*Inconclusive Election: Zaben-raba-gardama ne, ake sakewa inda adadin yawan kuri’un da aka yi rajista a rumfunan da aka soke kuri’u za su iya samar da ratar da ake bukata wanda ya yi na daya ya bai wa wanda ya yi na biyu. L