A daidai ana ta cece-kuce da kai ruwa rana a tsakanin jami’an hukumar zabe da wakilan jam’iyyar PDP a wajen bayyana sakamakon zabe, kwatsam sai ga shi jami’an tsaro sun taso keyar wani jami’in hukumar Zabe.
Shi dai wannan jami’in zabe ya bayyana karara cewa da shi aka hada baki aka zaftare wa jam’iyyar PDP har kuri’u 1000 a karamar hukumar Ade.
Da ya ke maida ba’asi, wannan jami’i mai suna Salau Mutiu ya ce shima umarni ne ya bi daga na gaba da shi.
Da ma can jam’iyyar ta karyata sakamakon zaben inda ta bayyana cewa sakamakon da hukumar zabe ta bayyana bai yi daidai ba da wanda suka shaida a rumfar zabe ba.
PDP ta sami Kuri’u 10836 a lokacin da aka kammala gidaya kuri’un, kowa ya sa hannu aka yi sallama aka watse. Sai kawai gashi kuma da ake ambato sakamakon wannan karamar hukuma sai gashi an zaftare Kuri’u 1000. Sailissafin ya koma 9836.
Mutiu ya ce bai kai ga yage ainihin takardar ta asali ba aka kama shi.
Sai dai kuma jami’an tsaro ba su yadda an shige da shi Mutiu cikin zauren da ake bayyana sakamakon zaben ba cewa kila hakan shiri ne don a wargaza aikin da ake yi a ciki wato bayyana sakamakon zaben.