GASAR CIN KOFIN ZAKARUN TURAI: Messi ya fara da kafar dama, Ronaldo da ta hagu

0

Fitaccen dan wasan kwallon kungiyar Barcelona ta kasar Spain, Leonel Messi ya fara buga wasan gasar cin Kofin Zakarun Turai ta kakar 2018/2019 da kafar dama.

Ranar Talata da dare ne Barcelona ta lallasa PSV Eindhoven ta Natheland da ci 4:0, inda Messi shi kadai ya kwarara kwallaye 3.

Can a Spain kuma washegari da dare a ranar Laraba, kungiyar kasar Italy ta birnin Turin, Juventus, ta yi tattaki har filin wasa na Mastella na kungiyar Valencia, inda suka daka wa masu gida dukan ci 2:0.

Dukkan kwallayen dai Pjanic ne ya ci su a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Sai dai kuma duk da wannan nasara da Juventus ta samu, sun koma gida da bakin ciki, domin alkalin wasa ya ba sabon dan wasan su, mashahurin nan da suka saya daga Real Madrid, Cristiano Ronaldo jan kati, a daidai minti na 29 da fara wasa.

Wannan jan kati ya girgiza hankalin Ronaldo matuka, domin shi ne jan kati na farko da aka taba bashi a tarihin wasannin sa na Champions League, sama da shekau 10.

An ba Ronaldo jan kati a daidai lokacin da bai fara nuna wata bajintar da aka yi tsammani zai nuna a Juventus ba, ganin cewa tun da ya je kungiyar, kwallaye biyu ya ci a gasar Seria A.

Har yanzu tsohon dan wasan Real Madrid na nan rike da tarihin sa wanda ba a taba ba shi jan kati ba a wasan Champions League da kuma La Liga.

Real Madrid mai rike da kofi ta fara da nasarar cin kwallaye 3:0 a kan Roma; Manchester United ta je har gida ta ci Young Boys na Switzerland da ci 3:0; Liverpool ta Ingila ta karbi bakuncin PSG ta Faransa, kuma ta kare mutuncin ta a gaban ‘yan kallo da ci 3:2; Ajax ta lallasa AEK Jenk ita ma da ci 3:0.

Manchester City ta sha kashi da ci 2:1 a gida, a hannun Lyon; Bayern Munich ta je har gida ta lallasa Benfica ta Portugal da ci 2:0.

Share.

game da Author