Sakamakon bincike da aka yi sun nuna cewa kwayoyin dafin ‘Tetanus’ wato Tsatsa kan yadu ta hanyar bin iska, ta inda idan aka yi wa yaro yanka a jiki idan ba an maida hankali ba ne zai iya kamuwa da cutar.
Kamar idan akayi wa yaro Kaciya, ko kuma wani karfe da bashi da kyau, da kuma abubuwan da ake yi wa yaro ko jarirai gashin cibi.
Hukumar kiwon lafiya ta duniya ta bayyana cewa bincike ya nuna cewa Najeriya na daga cikin kasashen duniya 18 da suke fama da wannan matsala.
A binciken an gano cewa kashi 20 bisa 100 na yara a Najeriya kan rasu a dalilan kamuwa da wannan cuta.
Bayan haka wani limami kuma mazaunin kauyen Kiyi dake Abuja mai suna Stephen Olusola, ya bayyana cewa rashin sani da rashin zuwa asibiti na cikin kalubalen da suke fama dasu wadda hakan ke sa cutar ya yi ta yaduwa.
” A wannan kauye na mu, mutane basu dauki zuwa asibiti yin awo ko haihuwa da muhimmanci ba. A ganin su abin alfahari ne idan har mace ta iya haihuwa ita kadai batare da taimakon kowa ba, wato ta haihu a gida.
Shi kuwa Nkwasi Nebo ma’aikacin cibiyar ‘PeachAid Medical Initiative’ya bayyana cewa rashin sanin mahimmancin yin allurar rigakafin wannan cuta na daga cikin abubuwan da ke sa ake kamuwa da cutar.
Nebo ya ce kamata ya yi duk mace mai ciki ta yi wannan allurar rigakafin cutar dafin tsatsa a lokacin da take zuwa awo asibiti sannan kuma suma jarirai idan aka haife su a tabbata an yi musu rigakafin cutar da zarar sun zo duniya.
Nebo ya kuma yi kira ga gwamnati da ta gina cibiyoyin kiwon lafiya kusa da mutane domin su sami saukin samun kulan da suke bukata.
Duk da kokarin da gwamnatin Najeriya ta ke yi wajen ganin an dakile yaduwar wannan cuta abin na neman ya fi karfin gwamnatin, sai dai kuma ana ba iyaye shawarwari game da matakan da zasu rika bi da kuma maida hankali domin gujewa fadawa matsala ifrin haka.
Ga shawarwarin a nan:
1. Yin allurar rigakafin dafin tsatsa, wato ‘Tetanus-Toxoid-Containing Vaccines, (TTCV)’.
2. Ana yi wa mace mai ciki domin kare dan da uwar daga kamuwa da cutar.
3. Mata su tabbatar suna tsaftace jikin su da ‘ya’yan su domin gujewa kamuwa da cutar.
4. A tabbata an yi rigakafin cutar.
5. Ana yi wa jariri allurar rigakafi na cutar akalla sau 3 tun yana jariri, sannan a yi masa kuma idan ya girma ya kai shekaru 15.