Wani soja mai mukamin sajen, mai suna Adegor Okpako, da ke tare da Bataliya ta 192 a Gwoza, ya kashe kan sa a misalin karfe 2:50 na ranar Laraba. Haka wata majiyar PREMIUM TIMES ta tabbatar da faruwar lamarin.
Kafin ya kashe kan sa, sai da Okpako ya harbe wani sojan shi ma mai mukamin sajen, wanda aka tabbatar da sunan sa Saka.
Bayan nan, kuma sai da ya ji wa wasu sojoji uku da wani dan CJTF mummunan raunuka a wani harbin kan-mai-uwa-da-wabi da ya rika yi, kafin ya harbe kan sa.
Okpako ya kashe kan sa kwanaki biyu bayan dawowar sa cikin bataliyar su, daga wani dan kwarya-kwaryan hutu da ya dauka na wasu ‘yan kwanaki.
Ba a san takamaiman dalilan sa na aikata wannan danyen aiki ba, ko kuma shin ya na fama da wata matsalar tabuwar kwakwarwa ce ko a’a.
PREMIUM TIMES ta yi kokarin jin ta bakin kakakin Hedikwatar Tsaron Sojoji da kuma sojojin dakile harin Boko Haram, an kasa samun su domin jin ta bakin su.
Sai dai su kuma hukumar sojojin, sun yayata a shafin su na tiwita can wajen 12 na daren jiya cewa sojan ba kashe kan sa ya yi ba, kuskure ne aka samu, bindigar ta tashi.
Sannan kuma sun tabbatar da mutuwar daya sojan da kuma raunin da sauran suka ji.
Daga nan sai samarwar ta kara da cewa za a gudanar bincike domin gano musabbabin tashin bindigar.
Amma kuma majiyar PREMIUM TIMES ta jajirce kan cewa lokacin da al’amarin ya faru, ba wani horaswa ake wa sojojin ba ko atisaye, kamar yadda hukumar sojoji ta nuna.