An cafke mai saida jabun dalar Amurka a Gombe

0

Rundunar Jami’an NSCDC na jihar Gombe ta bayyana samun nasarar cafke wani da ake zargin ya na saida jabun takardar kudin dalar Amurka.

Kakakin Yada Labarai na rundunar, Buhari Sa’ad ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke gudanar da taron manema labarai a Gombe jiya Laraba.

Ya ce an damke wanda ake zargin ne bayan da aka samu cikakken labarin abin da ya ke aikatawa daga jama’a.

Ya ce wanda ake zargin mai suna Augustine Samuel, an kama shi ya na dauke da takardar dalar Amurka guda 30, wadda kowace daya dala 100 ce.

Daga nan sai ya ce yawan safarar jabun dala da kuma yadda ake bayar da jabunta, abin damuwa ne kwarai a jihar. Daga nan sai ya ce rundunar su za ta kara tashi tsaye domin magance wannan matsala.

Sa’ad ya ce ana ci gaba da bincike, kuma ba da dadewa ba za a maka wanda ake zargin, mai shekaru 46 a kotu. Ya kuma yi kira da jama’a su ci gaba da ba su hadin kai domin a kakkabe batagari daga cikin al’umma.

Share.

game da Author