Ana bin mazauna garin Bauchi da kuma wasu kamfanoni bashin kudin ruwan sha na sama da naira bilyan daya. Haka Hukumar Bada Ruwan Sha ta jihar ta bayyana.
Aminu Gital wanda shi ne Shugaban Hukamar ta BSWSC, ya bayyana haka a lokacin da hukumar ta yi taro da wasu kamfanoni da kuma kungiyoyin sa-kai na jihar, a jiya Laraba.
Ya shaida musu cewa hukumar bada ruwan ta yi wa gidaje masu amfani da ruwan famfo sama da 22,000 rajista a cikin jihar, amma guda 1,020 kadai suka biya kudin ruwan famfo a kan kari.
“Kudin ruwan famfo a jihar Bauchi kusan ya fi na sauran jihohi sauki da rangwame, saboda naira 500 ake caji a duk wata a cikin unguwannin talakawa. Rukuninn gidaje na ‘estate’ kuwa ana karbar naira 750 a kowane wata. Sai GRA da ke biyan naira 1000 a kowane wata, amma duk da wannan rahusa da suke samu, sama da rabin masu amfani da ruwan famfo a jihar sai su ki biyan kudin ruwa” Inji Gital.
Ya ce wannan tauri-bashi ya dabaibaye hukumar sa da tulin matsalolin da ke kawo cikas wajen kasa samar da isasshen ruwan famfo ga dukkaninn kananan hukumomin jihar 20.
Sauran matsalolin da ke addabar hukumar inji Gital sun hada da tsadar gyara da kayann gyaran ijinan bada ruwa, biyan kudin wutar lantarki, sayen mai domin zuba wa janareto da kuma tsadar sinadarin tace ruwan famfo.
Ya ce zai haka kai da kungiyoyin sa-kai domin wayar wa mutane kai dangane da muhimmancin biyan kudinn ruwan famfo.