An tsinci gangar jikin wani dan sanda a Jos

0

An tsinci gangar jikin wani dan sandan mobayil a daidai sabon filin wasa da kwe kan hanyar Zaria, a garin Jos, cikin Karamar Hukumar Jos ta Arewa.

An tsince ta ne tun a ranar Asabar, amma jiya Laraba ne rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar.

Kakakin su Tyopev Terna ya tabbatar da cewa gangar jikin ta wani saje na ‘yan sanda ne da aka tura ya na aiki da Sashe na 1 na Opreation Safe Heaven.

“Kaftin na soja mai suna Joel Olanrewaju, ya kawo rahoto a ofishin ‘yan sanda na Laranto cewa sun samu gangar jikin wani saje na ‘yan sanda mai suna Unana Ishaya, wanda ke a aiki da Mopo 56 na STF.”

“Saje din ya bar inda suke aiki a ranar 1 Ga Satumba da yadda, da niyyar zuwa ya sayo suyayyen nama, amma shiru bai koma ba. An ajiye gawar a asibitin kwararru na jihar Filato, kuma ana ci gaba da bincike.

PREMIUM TIMES ta samu labarin cewa jama’ar yankin na cikin zaman fargaba tun bayan da aka samu gawar dan sandan.

A na su bangaren, ‘yan sanda na ci gaba da bincike a yankin domin gano wadanda suka kashe shi.

Wani jami’in Kasuwar Farar Gada da aka tsinci kan a kusa da su ya tabbatar da faruwar al’amarin.

Share.

game da Author