Kungiyar Manoman Shinkafa ta Najeriya (RIFAN), reshen Jihar Adamawa, ta bayyana cewa ambaliya ta yi tafiyar-ruwa da gonakin shinkafar manoma sama da 5000.
RIFAN ta cec wannan kuwa babbar barazana ce ga yalwar abincin da tun da farko ake ta murnar za a samu a kakar bana.
Shugaban Kungiyar ne na Jihar Adamawa, Mista Maduwa ya bayyana haka a lokacin da ya ke hira da manema labarai, ranar Litinin a Yola, jihar Adamawa.
Maduwa ya kara da cewa wadda ke da mabobi 7, 000 masu rajista a jihar, har yanzu ba ta kammala tantance iyakar munin barnar da ambaliyar ta yi wa manoma ba.

“Rahoton da ke zo mana daga kananan hukumomi da dama musamman daga wadanda ke kan gefen Kogin Benuwai, an tabbatar da ambaliya ta malale musu gonakin dubban manoma.
“Mun samu rahotanni da kananan hukumomin 16 daga cikin 21 na fadin jihar Adamawa, ciki har da Jada, Ganye da kuma Toungo.”
Daga nan sai ya ce mafi yawan manonan da ambaliya ta yi wa barna, duk ramcen kudade suka karba daga hannun gwamnati domin su yi noman shinkafar.
Sai yayi kira da kuma roko ga gwamnatin tarayya da ta tausaya musu, ta dubi halin da suke ciki.
Shi ma Babban Sakataren Hukumar Agaji ta Jihar Adamawa, Muhammed Suleiman, ya ce hukumar sa ta fara tantance adadin wadanda ambaliyar ta yi wa barna.
Ya kara tabbatar da cewa ruwan ya lalata gonaki dubban manoma.