Kotun Majistare da ke Minna, Jihar Neja, ta bada umarnin a tsare wani magidanci a kurkuku, saboda zargin sa ake yi da hannun a mutuwar matar sa.
Sai dai kuma wanda ake zargin mai suna Ilesanmi ya musanta cewa da hannun sa a mutuwar matar ta sa.
Mai gabatar da kara, Aliyu Malami, ya shaida wa kotu cewa wata mata ce mai suna Blessing Kunle ta kai karar Ilesanmi a Ofishin ‘Yan sanda na Suleja.
Malami ya ce wanda ake tuhumar ya gaura wa matar sa mai suna Patience kutufo, daga wani dan sabani da ya shiga a tsakanin su, a ranar 31 Ga Agusta, da misalin karfe 9:30.
Ya ce naushin da ya yi wa matar ta sa ya sa jini ya rika fitowa ta kunnuwar ta da kuma bakin ta, har aka garzaya da ita asibitin Suleja, inda ta mutu a can.
Mai Shari’a Ibrahim ya ki amincewa da ja-in-jar da Ilesanmi ya yi cewa kotun ba ta da hurumin sauraren karar ballantana a hukunta shi.
Daga nan sai ya bada umarni ‘yan sanda su yi kwafen karar guda su aika wa Daraktan Gabatar da Kararraki na Jiha, domin a nemi shawarar sa.
Ya ce a ci gaba da tsare wanda ake zargin har zuwa ranar 31 Ga Oktoba, ranar da za a ci gaba da sauraren karar.