Gwamnati ta rufe kamfanin gonakin Obasanjo a dalilin kin biyan haraji

0

Gwamnatin jihar Oyo ta rufe kamfanin gonakin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da wasu kamfanoni 12 a dalilin kin biyan kudin haraji da basu yi ba.

Hukumar haraji ta jihar ne ta rufe wadannan kamfanoni da gonaki.

Sauran wadanda aka rudfe sun hada da kamfanonin MRS Oil, Black Horse, Heinemann Educational Books, Lister Flour Mills, University Press Limited, Evans Brother, Brooking House, Group Medical Hospital, Butterfield Bakery, Chicken Republic da Rasmed Publicity.

Shugaban hukumar karbar Haraji ta jihar Mr Bicci Alli, ya bayyana cewa yin jala ya zama dole ganin cewa gwamnati ta dade tana yi wa wadannan kamfanoni tuni domin su biya harajin su amma suka ki.

Wannan aiki da suka yi ya shafi bankuna da ya hada da bankunan Diamond, Stanbic IBTC, Skye, FCMB, Heritage, Unity, Ecobank, UBA, Keystone, First Bank da Union Bank.

” Mun dade muna ta yi wa wadannan kamfanoni tuni kan kudaden haraji amma suka toshe kunnuwar kamar ba da su muke yi ba. Sannan kuma bamu saba wa doka ba hakan da muka yi.” Inji Alli

Share.

game da Author