Akawun majalisar dokoki ta Tarayya Sani Omonori ya sanar da daga ranar dawowar majalisar dokoki ta tarayya da ya hada da majalisar dattawa da na wakilai.
A wata takarda da ya fitar ranar Lahadi Omonori ya ce an yi haka ne saboda zabukan fidda ‘yan takara da jam’iyyun kasar nan za suyi a wadannan kwanaki.
Idan ba a manta ba majalisar kasa za ta dawo hutu ne ranar 25 ga watan Satumba.
Yanzu an daga dawowar zuwa 9 ga watan Oktoba kamar yadda sanarwan ya fadi.