A ranar Laraba ne jami’in hulda da jama’a na hukumar kula da alhazai na jihar Zamfara Yakub-Yahaya Talatan-Mafara ya sanar cewa an fara jigilar alhazan jihar daga kasar Saudiyya.
Talatan–Mafara ya fadi haka ne da yake ganawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Gusau.
Ya bayyana cewa jirgin farko ya sauka a tashar jiragen saman Sultan Abubakar III dake jihar Sokoto da karfe tara na safiyar Alhamis dauke da alhazai 552.
” Jirgin farko ya kwaso alhazan kananan hukumomin Bukkuyum, Birnin-Magaji, Kaura-Namoda, Zurmi da Tsafe.
Talata-Mafara ya ce bisa ga tsarin da suka yi jirgi na biyu zai taso daga Saudi ranar Alhamis sannan sauran alhazan da suka rage za su dawo gida ranar Asabar.