Kamfanin da ke kula da gonakin Obasanjo wato ‘Obasanjo Farms’ ya biya bashin Harajin da ake bin sa a jihar Oyo, har tuni an budi harabar kamfanin da aka garkame.
Shugaban hukumar karbar haraji ta jihar Oyo, Bicci Alli ya bayyana cewa babu kamshin gaskiya game da yayadawa da ake yi wai rufe gonar Obasanjo siyasa ce.
Alli ya ce sam ba haka bane. ” Aiki ne ya kai mu wannan wuri inda duk wanda ake bi bashi muka garkame ofisoshin su a jihar. Yanzu kamfanin gonakin Obasanjo din sun taho har ofis sun biya harajin su kuma mun bude ofishin na su. Babu abinda ya hada aikin mu da siyasa.
Idan ba a manta ba Gwamnatin jihar Oyo ta rufe kamfanin gonakin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da wasu kamfanoni 12 a dalilin kin biyan kudin haraji da basu yi ba.
Hukumar haraji ta jihar ne ta rufe wadannan kamfanoni da gonaki.
Sauran wadanda aka rudfe sun hada da kamfanonin MRS Oil, Black Horse, Heinemann Educational Books, Lister Flour Mills, University Press Limited, Evans Brother, Brooking House, Group Medical Hospital, Butterfield Bakery, Chicken Republic da Rasmed Publicity.
Shugaban hukumar karbar Haraji ta jihar Mr Bicci Alli, ya bayyana cewa yin jala ya zama dole ganin cewa gwamnati ta dade tana yi wa wadannan kamfanoni tuni domin su biya harajin su amma suka ki.
Wannan aiki da suka yi ya shafi bankuna da ya hada da bankunan Diamond, Stanbic IBTC, Skye, FCMB, Heritage, Unity, Ecobank, UBA, Keystone, First Bank da Union Bank.
” Mun dade muna ta yi wa wadannan kamfanoni tuni kan kudaden haraji amma suka toshe kunnuwar kamar ba da su muke yi ba. Sannan kuma bamu saba wa doka ba hakan da muka yi.” Inji Alli