Mazauna kauyukan Wanori, Kaleri da Amarwa da ke karamar hukumar Konduga sun ga tashin hankali ranar Laraba, bayan Boko Haram sun far musu cikin dare.
” Mun ga tashin hankali a garin Wanori. Wasun mu suna barci kawai sai muka ji harbi ta ko ina. Wasu sun gudu wasu kuma da Allah yayi kwanan su ya kare basu su sha ba.
” Bayan harbe-harbe da suka yi sun kwashe abinci da wasu kayayyakin mu sannan suka babbanka wa kauyen wuta.” Inji wani mazauna garin Wanori.
Wasu daga cikin mazauna Kauyukan Kaleri da Amarwa duk sun bayyana cewa yadda suka yi musu barin wuta sannan suka kwashe musu kayan abinci.
” Mu da Allah ya sa muka tsira mun tsira amma da yawa sun rasa rayukan su. Abin da ya taimaka mana shine zuwa dakarun sojin saman Najeriya da suka kawo mana dauki suka fatattaki wadannan ‘yan Ta’addan.
Hukumar bada agajin gaggawa ta Jihar da kwamishinan ‘yan Sandan jihar Barno sun tabbatar da wannan hari sannan sun ce jami’in tsaro tuni sun fantsama domin fatattakar su.
Discussion about this post