Har yanzu musulman Arewa na karkashin mulkin mallaka ne – Sarki Sanusi

0

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya yi kira ga gwamnatocin Arewa da su nemi a rika koyar da ‘Yan Arewa a jami’o’in yankin da harshen Hausa.

Sanusi ya bayyana haka ne a wajen taron kaddamar da wani fim da wata ‘yar kasar jamus mai suna Hannah Hoechner ta shirya da ke nuna yadda rayuwar Almajiri ya ke.

Sarki Sanusi ya ce kallon hadarin kaji da ake wa Almajirai da Almajiranci a kasar nan ya isa hakanan.

” A kasar nan an maida idan ka iya turanci shi kenan, ka zama jarumi wayayye mai ilimi, ba a ganin idan za ka iya rubutu da larabci ko karatu shima ilimi ne ko kuma shima wayewa ne.

” Bayan kuwa akwai ilimin Arabi sannan ana rubuta larabci da ajami ma shekaru 600 kafin zuwan turanci kasar nan.

” Dole ne fa musulmai su nemi ‘yancin su a kasar nan domin kuwa har yanzu musulunci na karkashin mulkin mallaka ne. Saboda ba a dauki al’adun mu da Harshen mu a bakin komai ba.

” Idan da za aka karanta littafan musulunci bila adadin, idan ba turanci ka iya ba ko ka karanta ba, ba a daukan ka a bakin komai a kasar nan.

” Sarkin Kano Muhammadu Rumfa tun a zamanin da wato tunkafin zuwan turawa ya kan aika mutanenzuwa kasar Barni, da Mauritania domin karatun Islama.

Sarki Sanusi ya kara da cewa a tun farko wani Rabaren ne mai suna Miller ya fara rubuta wa Lord Lugard wasika da a daina amfani da larabci da ajami a matsayin yaren da za a rika aiki da shi a Najeriya.

” Ku duba kasashe kamar su Egypt, China duk da harsunan su suke karantar da daliban su. Haka kuma ko a jihar Legas, an kirkiro dokar da dole sai ka ci darasin na yaren ‘yar banci sannan za ka samu damar shiga manyan makarantu mallakar jihar.

Yayi kira ga gwamnatocin Arewa da su kirkiro tsarin da zai ba da dama a rika karantar da ‘yan Arewa da harshen Hausa.

Share.

game da Author