Ganau ba jiyau ba ya tabbatar da cewa wani dan sanda a jihar Taraba ya bindige direba har lahira, saboda cin hancin naira 50 kacal.
Ganau din wanda ba ya so a ambaci sunan sa, ya ce sunan wanda aka bindige din Mohammed Dajji.
An bada rahoton bindige Dajji saboda ya ki ba dan sandan cin hancin naira 50, a daidai shingen ‘yan sanda da ke kauyen Maisamari, kusa da Nguroje.
Tsautsayin ya faru ne a yau Juma’a da misalin karfe 11:30 na safiyar Juma’a, kamar yadda PREMIUM TIMES ta samu tabbaci.
Bayan aikata kisan, mazauna kauyen sun yi taron-dangi kan dan sandan inda suka yi masa shegen duka.
Kakakin yada labaran ‘yan sanda na jihar ya ce shi ma yanzu ya ke amsa kira daga yankin, amma ba shi da takamaimen abin da ya faru.