Tsohon gwamnan jihar AkwaIbom Godswil Akpabio ya ziyarci tsohon gwamnan jihar Legas kuma jigo a jam’iyyar APC Bola Tinubu a gidan sa da ke, Abuja.
Idan ba a makon da ya gabata ne aka tsokata cewa Akpabio ya kammala shiri tsaf don komawa jam’iyyar APC daga PDP.
A dalilin wannan shiri ne ya ziyarci shugaban Kasa Muhammadu Buhari a kasar Britaniya inda yake hutun kwanaki 10.
Wannnan ziyara da aya kai gidan Tinubu daya ne daga cikin rangadin da yake yi wa shugabannin jam’iyyar kafin ya bayyana da kan sa cewa ya dawo jam’iyyar APC din.
Ba a fadi abin da ‘yan siyasan biyu suka tattauna ba.

Discussion about this post