Jami’an tsaron SSS sun yi wa kofar shiga Majalisa shinge.
Duk wani dan Majalisar Tarayya da ma’aikacin majalisar, an ana su shiga, an ce kowa ya koma gida.
PREMIUM TIMES ta samu labarin cewa wasu sanatoci 30 masu goyon bayan Buhari sun yi taro jiya da dare, tare da daraktan SSS, Lawan Daura, domin kitsa tuggun tsige Saraki.
Sannan kuma majiya mai tushe ta ce ana kokarin dora sanata Ahmed Lawan ne kan mukamin Saraki, sai kuma Hope Uzodinma a matsayin mataimakin sa.
Dama kuma jiya Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya gana da Ahmed Lawan.
Nayan an ya ta kai ruwa rana da wasu ‘yan majalisar da ga baya jami’an SSS din sun kyale ‘yan majalisan shiga ofisoshin su.
Wasu sanatocin da jami’an DSS suka yi wa shinge suka hana shiga majalisa, sun maida kakkausan martaninn yin tir da karfa-karfar da aka yi musu.
Sanata Rufai Ibrahim ne sanata na farko da ya fara isa bakin kofar shiga majalisar.
“Mun je bakin kofar shiga majalisa, da niyyar shiga ofis kamar yadda mu key i a kullum. Saboda dama ko lokacin da ake hutu, mu na zuwa domin yin ayyukan kwamiti da sauran rubuce-rubuce. Ni ina rubuta littafi, don haka a kullum ina shiga majalisa.
“Abin mamaki, mu na isa sai muka ga DSS sun yi dandazo a kowace kofar shiga majalisar. Wai sai suke ta yi mana burga cewa umarni ne aka ba su daga sama. Wato kawai a yanzu ‘yan takife sun rike wa dimokradiyyar Najeriya makogaro, ta fara kakarin mutuwa.
SANATA BEN BRUCE
Shi ma Ben Murray-Bruce, PDP-Bayelsa, ya yi Allah wadai da dandazon DSS
“Wato ana neman a nuna mana cewa ba za mu shiga Majalisa mu yi aikin mu ba, bayan majalisa ta tafi hutun zaman da ta key i kenan.
“Na nemi ofishoshin jakadun Amurka da Ingila su soke bizar Sanata Akpabio, wannan shi ne gogarman da ke jagorancin wannan harankazama tozarta dimokradiyya a wannan gwamnatin.
“Za mu nemi a soke bizar matayen su da ‘ya’yan su. Ba za a bari su bar kasar nan zuwa Turai ko Amurka ko kasashen Amurka ta Arewa ba.”
ISA MISAU
Sanata Isa Misau daga jihar Bauchi, ya bayyana wa manema Labarai a majalisa cewa har yanzu fa babu wani sanata dan jam’iyyar APC da ya bayyana a majalisa.
“Amma ina so in sanar muku cewa muna nan muna jiran su su zo, babu wanda ya isa ya tsige shugaban majalisar dattawa Saraki. Duk su gama kulle- kullen su.”
Honarabul Johnson Agbonayinma, da yake zantawa da manema labarai ya bayyana cewa abin da ya faru a majalisa yau ba wani abu bane illa neman a hana wasu yin aikin su.
Ya ce tabbas akwai shiri da ‘yan PDP suka yi na ganin an muzguna wa ‘yan APC a majalisar yau.