Hadurran mota ke sanadiyyar mutuwar kashi 95 bisa 100 na ‘yan bautar kasa

0

Hukumar Kula da ‘Yan Bautar Kasa ta bayyana cewa yawaitar hadarin mota ke sanadiyyar mutuwar kashi 95 bisa 100 na ‘yan bautar kasa.

Darakta Janar na Hukumar, Suleiman Kazaure ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke duba masu isa sansanin masu bautar kasa na Katsina, a yau Litinin.

“Da yawan masu bautar kasa na jefa kan su cikin tafiye-tafiyen da bas u da wani muhimmanci ko tasiri a rayuwar su, wanda sau da yawa sukan samu hadari har abin ya kai ga rasa rayuka.

“Rahotannin da ke a gaban Hukumar nan sun tabbatar da mace-macen ‘yan bautar kasa sun fi yawa ne daga hadurran da ke ritsawa da su sakamakon tafiye-tafiyen da bas u da wani amfani.

“Wannan yawan rasa rayuka kuwa kan faru ne saboda yawancin titinan kasar nan ba kyau gare sub a.

“Tun shekaru da dama a baya tititan kasar nan sun zama tamkar makabartar masu aikin bautar kasa. Don haka ‘yan NYSC su guji yawan tafiye-tafiyen da bas u da amfani sai fa idan kama tilas kawai.

Daga nan kuma sai ya yi kira ga wadanda ke da wani uziri na yin tafiya da su rika tuntuba da neman iznin jami’an NYSC.

Share.

game da Author