2019: Dankwambo ya kaddamar da takarar shugaban kasa

0

Gwamnan Jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo ya kaddamar da aniyar sa ta tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, a zaben 2019.

Dankwambo ya yi wannan kaddamarwar a gidan gwamnati, yayin da ya ke ganawa da jiga-jigan jam’iyyar karkashin jagorancin mataimakin jam’iyya na kasa, Babayo Gamawa da kuma dattawan jam’iyyar na jihohi shida da ke yankin Arewa maso Gabas.

Da ya ke magana ga jami’an jam’iyyar, Dankwambo ya ce ya amince da amsa kiran jama’a ne a fadin kasar nan na ya fito takarar a zabe mai zuwa na 2019.

Ya ci gaba da cewa ya yanke shawarar fitowa takarar ne domin ya ceto kasar nan daga yunwa da fatara.

Daga nan sai ya ce idan za a yi adalci, yankin Arewa maso Gabas ya kamata ya samu shugabancin kasar nan haka nan. “Domin rabon yankin Arewa da shugabanci tun zamanin Tafawa Balewa”, da aka kashe a yunkurin juyin mulkin 1966.

A karshe ya ce Najeriya na bukatar gwarzon dan siyasa, kuma shugaban da ya samar wa jama’ar sa ci gaba da kuma sanin dabarun inganta tattalin arziki, wanda ya yi aiki da kwarewar ta sa, kuma aka gani, aka tabbatar kamar shi.

Share.

game da Author