Saraki ba zai sauka daga shugabancin Majalisa ba -Sanata Misau

0

Wasu sanatoci sun maida wa Sanata Abu Ibrahim da saurran sanatocin APC martani cewa kada ma su sake su tayar da hatsaniya idan Majalisar Dattawa ta dawo a ranar 25 Ga Satumba.

Sanata Isa Misau daga Bauchi da Sanata Rafiu Ibrahim ne suka yi wannan gargadi dangane da wata hira Sanata Ibrahim da aka yi da shi a jaridar The Cable. Sun ce muddin su Abu Ibrahim suka nemi tayar da husuma, to za su gamu da daidai da su.

Su na magana ne a kan zargin da aka yi cewa sanatocin APC za su yi amfani da jami’an tsaro a tsige Sanata Saraki.

“Irin kalaman da Sanata Abu Ibrahim ya yi a cikin hirar da aka yi da shi, ya nuna cewa shi da abokan shirya tuggun sa ba cikakkun ‘yan kishin dimokradiyya ba ne. Ba su yi amanna da bin doka da oda ba, kundin tsarin mulki da kuma ka’idojin Majalisar Dattawa.” Inji su.

“Ta yaya wanda ke kishin dimokradiyya zai yi irin wannan kasassaba, har ya ce wai za su hargitsa zaman majalisa, don kawai sun rasa mambobin su kuma yanzu sun koma yi wa majalisa barazana?

“Kalaman sa sun nuna dalilin da ya sa daya daga cikin su ya shiga da ‘yan daba har cikin zauren majalisa har suka sace Sandar Mulkin Majalisar Dattawa.”

Sanatocin sun kuma nuna takaicin yadda har yau gwamnati ba ta bari an hukunta wadanda suka saci sandar mulkin ba.

“Kasancewar Abu Ibrahim shi ne shugaban Kwamitin ‘Yan sanda a Majalisar Dattawa, hakan ya sa ba mu yin mamakin yadda ake zargin yin amfani da ‘yan sanda domin biyan bukatar bangaren gwamnati.”

A karshe wadannan sanatoci biyu sun jaddada cewa idan su Abu Ibrahim suka yi amfani da karya doka a majalisa, to su kuma za su yi amfani da doka su karya musu fukafiki.

Share.

game da Author