EKITI: Dan takarar PDP ya daukaka karar zaben gwamna

0

Dan takarar zaben gwamnan jihar Ekiti na jam’iyyar PDP, Kolapo Olusola, ya daukaka karar sakamakon zaben gwamnan jihar wanda aka gudanar a ranar 14 Ga Yuli, 2018.

Olusola wanda shi ne mataimakin gwamna mai barin gado, ya daukaka karar ne a gaban a Ado Ekiti, babban birnin jihar, inda ya bayyana cewa shi ne ya fi samun halastattun kuri’u masu yawa fiye da Kayode Fayemi, dan takarar APC, wanda ya kayar da shi.

Tuni dai Hukumar Zabe INEC ta damka wa Fayemi katin shaidar cin zaben, wanda ya samu kuri’u 197,459, yayin da Olusola na PDP kuma ya samu 178,121.

Za a rantsar da Fayemi a ranar 6 Ga Oktoba, 2018.

Olusola ya isa Kotun Sauraren Kararrakin Zabe da ke cikin Babbar Kotun Jihar Ekiti tare da wanda ya yi masa takarar mataimaki, Kazeem Ogunsakin da misalin karfe 5: 15 na yamma.

Ya bayyana cewa zamanin Fayemi idan ma an rantsar da shi, ba zai yi karko ba, domin PDP na da kwararan hujjojin da za su kayar da shi a kotu.

Wani babban lauya mai matsayin SAN ne mai suna Yusuf Ali zai ja tawagar gungun lauyoyin da za su jagoranci karar da ya shigar.

Tuni dai shi da wadannan lauyoyi suka gabatar wa kotu da shafuka 700 na kundin da suka tattara hujjojin da ya ce za su kayar da APC a kotu.

Dama cikin bayanan shigar da karar ya nemi kotu ta soke nasarar Fayemi ta bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara.

Share.

game da Author