TAMBAYA: Menene Ilimi a musulunci, akwai wanda addini ya hana a neme shi? Tara da Imam Bello Mai-Iyali

0

AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi
Muhammad SAW.

A musulunce ilimi shi ne sani kuma kishiyar jahilci, wato riskar ko
fahimtar abu akan hakikaninsa cikin yakini. Sannan a musulunce ilimi ya kasu gida biyu: Ilimin Addini (shari’ah), da Ilimin rayuwa. Amma ilimin addini shi ne ilimin sanin Allah da bautamasa, wanda Allah ya saukar kuma annabi Muhammad Salallahu Alaihi wa Sallama yayi
bayaninsa. Ilimin rayuwa kuwa shi ne duk wani ilimi mai amfani don inganta rayuwar dudiyarsa.

Neman ilimin addini ko na rayuwa yana zamowa farali a kan kowa (FARDU AIN) kuma yana zamowa faralin da idan wasu suka tsayo da shi (FARDU KIFAYA), to sauran mutane sun tsira.

Ma’ana shi ne wajibin kowane da yasan Allah da yanda zai bautamasa, kuma ya kware akan ilimin sana’arsa.

Duk ilimi mai amfani ne matukar musulmi ya tsare dokokin Allah a cikinsa, kuma yayi amfani da ilimin wajen bautar Allah da bunkasa al’umma. Kuma ya nemi ilimin da IKHLASI ga Allah,to yanada lada akan
wannan ilimi ko wane irine.

kuma yayi aiki da hadisin Annabi da yayi
umurni da neman ilimi.

Ilimi a karan kansa baya zama Haramun saidai hanyar neman ilimin ko aiki da ilimin ko wasu abobuwan da aka gurbata
ilimin dasu, su haramta ilimin, ko kuma ma mutumin da zai nemi wannan ilimin bai cika ka’idar neman wannan ilimi ba, da sauran dalilai na halin yau da gobe na zamantakewar mutane, duk sukansa shari’ah ta haramta kuma ta hana neman wani nau’i na ilimi.

Misali: Ilimin SIHIRI, tsafi, bokanci tsubbace-tsubbace ko kulumboto, ilimi ne da ke kai mai shi zuwa ga shirka don haka haramun ne.

Amma kuma wani masanin irin wannan ilimi zai iya taimakawa wanda aka cutar ta wannan hanya, ta amfani da ilimin ta hanya mai kyau.

Ya tabba cewa sahabai suna tambaya domin neman sanin sharri, amma badon su yi sharri ba, saidai don su kare kansu daga sharri mai sharri.

Shari’ah ta haramta kuma ta hana neman duk ilimin da zai kai mutum zuwa ga halaka ko shirka ko cutatar da al’umma ko cutatar da kansa.

A kan ma’aunin LA DARARA WALA DIRARA (ba cuta ba cutarwa). Sannan hukuma na iya hana neman wasu ilmomi ko da kuwa halal ne sabo da illolinsu ga al’umma.

A musulunce a kwai wasu ilmomi masu hadari kwarai kamar Ilahiyat: wato
ilimin hakinin zatin Allah da Ilimin sihiri/tsubbu, ilimin badini, Ilimin madiqi,.

Sannan a zamanacen ma akwai wasu ilmomi masu hadari kwarai musamman idan mutum zai karance su ta hanyar karatun Boko kamar: Ilimin philosophy, Ilimin Law, ilimin economics, ilimin pshycology, dole ne dalibai su rike imaninsu kuma su tsaya akansa, duk abinda ya sabawa AQIDA ta musulunci, toh, su yi Imani da na musulunci ko da kuwa za suyi aiki da wacan akan lalura.

Allah shi ne mafi sani.

Amsoshin Tambayoyin ku

Share.

game da Author