Kungiyar kare hakkin a musulmai (MURIC) ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta dauki darasi daga kasar Ghana game da kafa wuraren kiwo wa makiyaya a kasar a matsayin hanya na kawar da tashin-tashinan da yaki ci yaki cinyewa tsakanin makiyaya da manoma.
Shugaban kungiyar Ishaq Akintola ya bayyana haka ranar Litini inda ya kara da cewa daukar wannan mataki zai taimaka wajen samar da mafita ga wannan matsala.
” A kasar Ghana an sami irin wannan matsalar sai dai kuma su sun kafa wuraren kiwo ne, suka killace fulanin kasar ta inda ba za su sami irin matsalolin da muke fama dasu a kasar nan.
Ya kuma kwabi bangarorin gwamnatin kasar nan tare da gidajen yada labarai da kowa ya maida hankali wajen samar da tsaro a kasar nan sannan a hada hannu wajen ganin ba a kyale gwamnati ba kadai da samar da tsaro.