Shugaban asibitin Yariman Bakura dake Gusau jihar Zamfara Bello Mohammed ya koka kan yadda fannin kiwon lafiyar jihar ta rasa likitoci sama da 20 a cikin watanni shida.
Bayan haka kwamishinan kiwon lafiya na jihar Zamfara Lawal Liman ya bayyana cewa gwamnati ta fara gyara cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a jihar.
Liman yace gwamnati na yin haka ne domin inganta fannin kiwon lafiya na jihar saboda mutanen karkara da sauran masu bukatar kiwon lafiya.
Ya ce a yanzu haka gwamnati ta fara gyara asibitoci 15 daga cikin 147 din dake jihar.
Discussion about this post