Dogara ya kaurace wa taron ganawar wakilan APC da Oshimhole

0

Kakakin Majlisar Tarayya, Yakubu Dogara, ya kaurace wa taron da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya gudanar da mambobin wakilan majalisar tarayya da ke karkashin tutar APC.

Dogara ma dai ana sa ran zai tsallake APC ya koma PDP, kuma a ranar Talatar da ta gabata ne ya jagoranci zaman majalisar da ya bayyana sunayen wakillan APC 36 da suka koma PDP.

Shugaban Masu Rinjaye, Femi Gbajabiamila ne ya jagoranci sauran a ganawar da suka yi da Osinbajo.

Gbajabiamila ya tabbatar wa Osinbajo cewa wadanda suka canja sheka ranar Talata, za su dawo APC nan ba da dadewa ba.

Ya kuma roki APC da ta bayar da tikitin sake tsayawa takara na kai tsaye ga ‘yan majalisa da ke a kai yanzu.

Ya ci gaba da cewa a ganawar da suka yi shugaban jamiyya Adams Oshimhole, sun tattauna matsalolin da suka dabaibaye jam’iyyar APC.

Gbajabiamila ya ce an kira taron ne domin a jinjina wa mambobin da ba su fusata sun canja sheka ba.

Daga nan sai ya ce har yanzu APC ce ke da rinjaye a majalisar, sannan kuma ya roki da a jawo wadanda ba su canja sheka ba a jika.

Da ya ke ganawa da manema labarai bayan ganawar su da Osinbajo, Gbajabiamila ya kara da cewa haduwar ta su da mataimakin shugaban kasa ta yi tasiri sosai, domin ya na da yakinin cewa wadanda suka fusata suka fice din duk za su dawo.

Share.

game da Author