Shugaba Muhammadu Buhari ya jaddada cewa babu wanda ya fi karfin hukuma ta bincike shi a fadin kasar nan.
Ya yi wannan jawabi ne a cikin jawabin sa kakakin sa Garba Shehu ya sa wa hannu.
Ya yi jawabin ne biyo bayan korafe-korafen tir da tofin Allah-wadai da aka rika yi bayan ‘yan sanda sun kai farmaki a gidajen Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki da Mataimakin sa Ike Ekweremadu.
Ya ce duk da dai babu ruwan fadar sa shiga harkar jami’an tsaro, duk da haka ya kamata a kyale hukuma ta rika yin aiki kan binciken duk wani da ake zargi da aikata laifi komai girman sa.
Sai dai kuma kwanaki 19 kenan tun bayan da PREMIUM TIMES ta fallasa Ministar Harkokin Kudade, Kemi Adeosun cewa ta mallaki takardar shaidar sahale mata aikin bautar kasa, ta bogi, har you Buhari bai ce komai a kan ta ba.
Jama’a da dama a fadin kasar nan su na ci gaba da kiraye-kirayen Buhari ya sauke Kemi kuma ya sa a yi kwakkwaran bincike.
Kungiyoyin rajin kare talakawa da na ‘yancin jama’a da sauran su na ta matsa wa Buhari lamba kan a binciki harkallar Kemi.
Wasu ‘yan adawa kuma sun fara cewa idan ba a bincike ta an hukunta ta ba, to Buhari ya daina kururuwar yaki da rashawa da cin hanci kawai, tunda abin na sa kan masu adawa ya ke karewa kawai.