Wani lamari da ya ke neman yamutsa majalisar wakilai da ta dattijai nan da wasu makwanni masu zuwa, shine batun kudurin nan da mataimakin majalisar dattajai Sanata Ekwemeradu ya gabatar, don ganin an kirkiro ‘yan sandan jahohi a Najeriya.
Duk da cewar kudurin ya wuce karatu na farko, yana kokarin samun na biyu, amma da yawa daga cikin wasu ‘yan majalisu sun fara adawa da shirin, domin ko a satin nan, naga Sanatan da ke jagorantar kwamitin ‘yan sanda a majalissar ta dattawa Sanata Abu Ibrahim yana ikirarin ba inda kudurin zai je.
A gaskiya idan har za ayi duba na tsanaki da nutsuwa dangane da wannan lamari, dole a dakatar da batun.
Don kasashe irin su Faransa, Amurka da su Jamus suna da wannan tsari, to balagar wayewa, siyasa, da sanin makomar aiki irin ta dan sanda da ma Najeriya, ba su kai munzalin da za mu yi haka ba a yanzu. Tamkar ma za a kara jefa kasar cikin wani lamari ne na rudani da rashin tabbas.
Ku duba dai ku ga yanda gwamnoni ke yamutsa nutsuwar duk wasu da za su yi adawa da su a gwamnati, ko da kuwa a cikin jam’iyya daya suke. A Yanzu haka gwamna zai iya sawa aje a kamo mutum ayi masa duk abin da ake so, kuma ba mai bin kadinsa. Wata kila aji hukumomin rajin kare hakkin mutane suna ta babatu a kafafen sadarwa.
Da yawa daga gwamnoni, musamman a yankunan da ake fama da rikici na kabilanci, anan ma gwamna zai iya cin zarafin masu rauni ko wadanda ba ya so.
Jahohi nawa ne a yanzu da ba sa iya biyan ma’aikata hakkokinsu, kusan malaman makaranta bayin Allah? Kuma me ake zato idan ma’aikatan tsaro sun fada cikin matsin rayuwa, saboda rashin albashi, irin malamai?
Yana dai da kyau mu yi nazari mai zurfi. Duk wannan yamutsi da tashin-tashina da ake fama da su, akwai sakaci da kawar da kai, gami da rashin hukunci daga gwamnati. Da masu daukar nauyi, da masu yi, da masu karesu idan sun yi, duk za a iya mamayarsu, hukunci ya bi ta kansu ta hanyar shari’ah.
Ya kamata hukuma ta mike sosai. Adalchi da daidaito shine tushen zaman lafiya, ba wai batun kirkire-kirkiren wasu hukumomi da bangarorin tsaro ba!
Discussion about this post