Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya bayyana halayen Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin mutum mai gaskiya, mai kishin kasar sa Najeriya, fiye da yadda ya ke kishin kan sa.
Ganduje, wanda shi ne gwamnan jihar da Buhari ya fi samun yawan kuri’u a zaben shugaban kasa na 2015, yace Buhari wani tambari da hatimi ne na gaskiya da rikon amana, ya na karin bayani cewa, “Samun Buhari a shugabancin kasa, wani gagarimin dace ne da shugaba mai gaskiya da kishin kasa.”
Ya yi wannan jawabi ne a jiya Litinin a wurin walimar cin abincin da shugabannin jam’iyyar APC na Shiyyar Kudu-maso-gabas suka shirya masa a Owerri, babban birnin jihar Imo.
Duk da wannan zuga da kambamawa da Ganduje ya rika yi wa Buhari, shugaban kasar bai samu halartar taron walimar ba.
Yabon na kunshe ne cikin wata takardar manema labarai da Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamna Ganduje, Malam Abba Anwar ya fitar, yau Talata da sanyin safiya.