Shawarari 12 ga shugaba Buhari da ‘Yan Najeriya, Daga Mustapha Soron Dinki

0

Kafin a gyara matsala a duk inda take akwai bukatar a samu ilimin sanin tushen ta da gangar jikin ta da kuma rassanta don a san ta inda za’a soma gyaran.

Misali, matsalolin kasa (country) kamar matsalar gidan ka ce wacce take samun asali ko dai daga wajenka kai maigidan ko kuma daga wajen matar ka ko kuma ya kasance daga bangarori guda biyun.

Idan kuma ba haka ba, akwai wadanda daga nesa suke kunno maka wuta a gidan saboda haka idan za’a gyara Najeriya inaso a duba wadannan shawarwari guda goma sha biyu ko zasu yi aiki:

1 – Tabbas sai an fara canja al’adar siyasar Najeriya sannan za’a samu ci gaba. Canji daga siyasar kudi da sara-suka da kuma sace-sace zuwa siyasar adalci da farin ciki.

2 – A ci gaba da yaki da cin hanci da rashawa na adalci koda za’a cinye zangon mulkin farko akansa kadai.

3 – Ayi kokari a ‘dan lasawa talakawa zuma kafin wancen babban rabon yazo.

4 – Wajibi ne a jajirce wajen yin aiki da doka koda kotu zata daure kowa a Najeriya saboda a samu adalci ga kowa tsakanin talaka da mai mulki.

5 – Akwai bukatar talakawan Najeriya su ce duk wanda zai yi takarar dan majalisar tarayya sai anyi hirar awa daya dashi a gidan radio ko TV da turanci saboda a samu wakilci nagari.

6 – Dole sai ‘yan Najeriya sun daina ci-da-zuci don babu kasar da ta ci gaba a shekara hudu. Badaqalar Najeriya tafi karfin a gyara ta a shekara ashirin ma sai dai a rage mata karfi kawai.

7 – Gwamnatin Najeriya tana bukatar shigo da matasa cikin siyasa da mulki da gudanarwa saboda su zama kwararrun shugabannin yau da kuma gobe.

Sai an samar da juyin-juya-hali a tsarin ilimin kasar mu da kasuwar aiki (Job market) domin sune suke fara ‘frustrating’ matasan Najeriya.

9 – Sai jam’iya mai mulki ta dauke kan ta daga ‘ya’yanta da aka same su da cin hanci da rashawa don ci gaban Najeriya.

10 – Dole sai talakan Najeriya ya samu izzar cewa kuri’arsa tafi bakin bindiga tsorata dan siyasa a filin zabe don haka ya rike ta da mahimmanci.

11 – A daure a bawa INEC damar tayi dokar cewa duk dan takarar da aka gani yana yawo da ‘yan sara-suka ba zai yi takara ba saboda wannan siyasar jahiliya ce irin ta da.

12 – Lallai sai mun yi imani da cewa gyaran Najeriya a hannun Allah yake ba bawan sa ba. Allah ne kawai yake tabbatar da abu ta sababin bawansa.

Nasan wasu zasu ce Soron dinki ya kwasota da zafi, gaskiya gyaran wadannan matsalolin zai dauki lokaci amma idan akwai tsarkin zuciya tsakanin ‘yan Najeriya da shugabaninsu abu ne mai sauki a tabbar da gyaran. Sai dai akwai bukatar hakuri da addu’a don hakuri rabin nasara ne a cikin rayuwa.

Allah yasa muga alheri.

Share.

game da Author