Yadda Shema ya karkatar da kudaden Kananan Hukumomi – Mai shaida

0

Wani mai bada shaida a ci gaba da shari’ar da ake yi wa tsohon gwamnan Jihar Katsina, Ibrahim Shema, ya bayyana yadda tsohon gwamnan ya rattaba amincewa a kashe kudaden kananan hukumomin jihar a tsakanin 2013 da 2015, ba tare da bin ka’idar da doka ta gindaya ba.

Ibrahim Bujawa ne ya yi wannan cikakken bayani ga Hukumar EFCC, kuma aka gabatar da kwafen bayanin na sa a gaban kotu, a matsayin shaida mai lamba 2.

Mai shaidar, ya yi bayanin cewa kwamitin da aka nada domin ya binciki yadda aka kashe kudaden, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin, ya gano cewa an bi wasu hanyoyi aka yi asarkala da kudaden.

“Ni aka dora shugaban kwamitin da zai binciki yadda aka kashe kudaden Hukumar Ilmi a Matakin Farko ta Jihar Katsina, wato SUBEB. Kuma mun binciko yadda aka rika karkatar da kudade ba bisa ka’ida ba. Wasu kudaden a kan fallen warkar takarda ake bada umarnin a fitar da su daga Asusun Hadin Guiwa na Jiha da Kananan Hukumomi, wanda ke karkashin kulawar Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu ta jiha.

“Kudaden da muka gano sun salwanta za su kai maira biliyan 34.” Inji Ibrahim Bujawa mai bada shaida.

Ya ci gaba da rattaba cewa da yawan kudaden an rika karkata su ko kuma an rika fitar da su ne zuwa asusun Kungiyar Shugabannin Kananan Hukumomi ta Jiha (ALGON), wadda kungiya ce kawai ba hukuma ba.

Gungun masu kare Shema a karkashin jagorancin babban lauya J.B Daudu, A.T Kehinde, B.Y Kura da kuma Uyi Igunma, sun ki amincewa da kwafen takardar bayanan da ke kunshe wadanda Ibrahim Bujawa ya yi wa EFCC.

Sai dai kuma kotu ba ta saurari kiran sun a kada a karbi rubutaccen jawabin da Bujawa ya yi wa EFCC a matsayin shaida ba.

Tun da farko dama sai da mai gabatar kara ya tambayi Bujawa, shin ko kwamitin da ya ce ya shugabanta sun gudanar da bincike, halastaccen kwamiti ne? Kuma nada shi aka yi, ko shi ya nada kan sa?

Bujawa ya masa da cewa kwarai halastacce ne, kuma gwamnatin jiha ce ta nada shi.

Har ila yau, Ologunorisa mai gabatar da kara, ya tambayi Bujawa shin idan ya ga takardar da ya rubuta bayani a gaban EFCC zai iya gane ta?

Bujawa ya amsa ya ce kwarai zai iya gane rubutun sa.

Daga nan sai Ologunorisa ya mika takardar a gaban sa, shi kuma ya ce kwarai rubutun sa ne.

Mai Shari’a ya amince da ajiye takardar a kotu, a matsayin shaida.

Daga nan sai Mai Shari’a Bako ya daga sauraren karar zuwa 9 Ga Yuli da kuma 10 Ga Yuli, domin a zartar da ko takardun sun samu karbuwa a matsayin shaida a kotun ko a’a. Daga nan kuma za a ci gaba da shari’a.

Ana tuhumar Shema tare da wasu mutane uku, Ibrahim Lawal Dankaba, Sani Hamisu Makana da kuma Ahmed Rufai Safana da yin almubazzaranci da naira biliyan 11 daga cikin kudaden asusun ajiyar kananan hukumomin jihar Katsina.

Share.

game da Author