Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana tabbatacin cewa bai yiwuwa duk irin tuggun da mai tuggu zai kulla har ya murde zaben Gwamnan Jihar Ekiti.
Za a yi zaben gwamnan jihar Ekiti ne a ranar 14 Ga Yuli.
INEC ta ce irin fasahar zamani da ta ke amfani da su ne ya sa murdiya ko magudi ba zai yiwu ba.
Dama a cikin makon da ya gabata, INEC ta ce magudin zabe da murdiya sun zama tarihi a Najeriya.
Hukumar ta ce ba gaskiya ba ne yadda wasu ke ta yada jita-jitar cewa za a yi magudi a zaben Ekiti. INEC ta ce wannan maganganu ne marasa tushe kawai.
Kwamishinan INEC na jihar Ekiti, Abdulganiy Raji ne ya bada wannan tabbacin a ranar Talata yayin da ake taron wayar da kai kan zabe mai zuwa na gwamnan jihar Ekiti.
INEC ta sa wa taron suna, ‘Zabe ba fada ba’, an shirya shi ne domin kara wayar wa matasa kai dangane da muhimmancin gudanar da zabe lami lafiya.
Cibiyar Nazarin Dimokradiyyta ta kasa ce ta dauki nauyin shirya taron tare da UK Aid da USAID.
Ya ce tsarin zaben duk ya na cikin kwamfuta, kuma ba’arin jama’a da dama na kallon duk yadda jefa kuri’ar ke wakana ta na’ura mai kwakwalwa.
Ya ce wannan tsari ya samarwa kuri’un da za a kada tsaro sosai, ta yadda ba za a iya baddala su, a kara su ko a rage su, balle har a yi magudi koma murde su ba.
Daga nan sai ya yi kira ga duk wanda bai karbi katin shaidar damar yin rajista ba, to ya garzaya ya karba.
Ya na mai cewa INEC babu ruwan ta da goyon bayan kowa, duk wanda aka zaba da mafi rinjayen kuri’u shi ne zai yi nasara.
“Ya kamata a zabe a cire son rai, tashin hankali da rikice-rikice. Zabe ba ko-a-ci-ko-a-mutu-ba-ne. Tilas mutum daya ne zai yi nasara.
“Mun gudanar da zabe lami lafiya a shekarar 2014 a jihar Ekiti. Amma sai mutane suka famjama kone-kone da kashe-kashe bayan zabe.
Wannan karo mu na kira ga mutane da su bi doka, su nuna da’a da kamun kai a lokacin zabe da bayan zabe.”
A karshe ya tabbatar da cewa za a kare dukiyoyi, lafiya da rayukan jama’a sosai a lokutan zaben da za a gudanar a ranar 14 Ga Yuli.
Discussion about this post