A dai na shelar cewa an sami nasarar kawar da cutar Ebola a Kongo sai an tabbatar – WHO

0

Shugaban kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) Tedro Ghebreyesus ya gargadi ma’aikatar kiwon lafiyar kasar Kongo da su guji yin hazarin sanar da nasarorin da suka samu a yakin da suke yi da bullowar cutar Ebola a kasar.

Ghebreyesus ya gargadi ma’aikatan kiwon lafiyar kasar Kongo a ziyar da ya kai Kinshasa babban birnin kasar.

Kamata ya yi sai an sami tabbacin kawar da cutar tukuna kafin su sanar da kawar da cutar.

” Ko da yake ba mu tabbatar da ingancin wannan maganin ba amma a wannan karo da cutar Ebola ya bullo a kasar Kongo maganin ya taimaka mana matuka batare da mun samu matsaloli ba’’.

” Sai dai yayin da ake haka ma’aikatan kiwon lafiyar kasar sun rawaito cewa cutar ta sake bullowa a kauyen Iboko a cikin makon da ya gabata duk da cewa mun yi wa mutane 2,200 allurar rigakafin da zai kare su daga kamuwa da cutar.

“Sanadiyyar haka ya sa nake gargadin mu duka da mu iya wa bakin mu har sai mun sami nasarar kawar da cutar gaba daya daga kasar kafin mu ce wani abu’’.

Share.

game da Author