Duk da bakin talauci da ayyukan masu garkuwa gwamnatin Zamfara ta biya wa jami’an ta 5 su je kallon ‘World Cup’ a kasar Rasha

0

Sanin kowa ne cewa jihar Zamfara tayi kaurin suna wajen ayyukan masu garkuwa da mutane da barayin shanu in da sai kaga an kaiwa kauyuka da dama hari, an kashe na kashewa an sace na sace wa.

Bayan wannan fitina da ya addbi mutanen jihar, Jihar na fama da tabarbarewar kiwon lafiya da ilimi matuka.

Idan ba a manta ba akwai lokacin da ministan lafiya ya yi kira ga gwamnan jihar AbdulAziz Yari da ya maida hankali wajen samarwa da inganta cibiyoyin kiwon lafiya a fadin jihar.

Kwatsam sai gashi kwamishinan matasa da wasannan ya bayyana cewa gwamna Yari ya amince masa da wasu jami’an gwamnati 4 su tafi kasar Rasha domin kallon wasan kwallon kafa na cin kofin duniya da za a fara ranar 14 ga wannan wata.

Kwamishina Abdullahi Gurbin-bore ya ce a matsayin sa na kwamishinan matasa da wasanni, tuni gwamna ya amince masa da ya ziyarci kasar Rasha din don kallon wasan da wasu jami’an gwamnati biyar da duk a aljihun gwamnatin jihar za a ayi amfani da.

Bayan shi akwai mai ba gwamna shawara kan harkar wasanni, darekta janar na wasan kwallon da shugaban kungiyar kwallon kafa ta kasa na

Share.

game da Author