Mutanen garin su Abiola na so a kara wa Buhari wa’adin mulki

0

Basaraken mahaifar marigayi MKO Abiola, wanda ya lashe zaben 12 Ga Yuni, 1993, ya yi kira da a kara wa Shugaba Muhammadu Buhari wa’adin kwanaki 14 bayan kammala zangon san a 2019.

Ya yi haka ne domin su na so a rantsar da shugaban da ya yi nasara a zaben 2019 a ranar 12 Yuni, 2019, tunda ita ce ranar da Buhari ya maida ranar Dimokradiyya.

Tun bayan da aka rantsar da Olusegun Obasanjo a matsayin shugaba a ranar 29 Ga Mayu, 1999, sai aka maida Mayu 29 a matsayin ranar dimokradiyya, kuma ita ce ranar da ake rantsar da sabbin shugabanni a matakin kasa da jihohi.

Sai dai kuma basaraken Gbagura, cikin jihar Ogun, garin da aka haifi Abiola, ya bayyana wa manema labarai cewa ai ya zama tilas a maida ranar mika mulki ta koma ranar 12 Ga Yuni, domin ta hakan ne za a kara tabbatar da sahihanci da karbuwar zaben na 12 Ga Yuni, 1993 da nufin raya fafutikar da MKO Abiola ya yi, wadda ita ce sanadin ajalin sa a tsare.

Cikin makon jiya ne Gwamnatin Tarayya ta bai wa Abiola kyautar babbar lambar girmamawa ta GCFR, kuma ta maida ranar 12 Ga Yuni ranar dimokradiyya, maimakon ranar 29 Ga Mayu.

Majalisar Tarayya ta amince da wannan hobbasa da Gwamnatin Tarayya ta yi, sannan ta nemi a kaddamar da Abiola a matsayin tsohon shugaba kasa, kuma a biya shi dukkan wani hakki da ya wajaba a ba shi.

Sun kuma nemi INEC ta bayyana Abiola a matsayin wanda ya lashe zaben 12 Ga Yuni, 1993.

Share.

game da Author