Yadda Trump da Kim suka kafa babban tarihi a duniya a taron Singapore

0

Shugaban Amurka Donald Trump da takwaran sa na kasar Koriya ta Arewa, Kim Jong-Un sun yi taron ganawa na farko a tsakanin shugabannin kasashen biyu, tun bayan Yakin Duniya na Biyu.

Sun yi wannan ganawa ce kokarin da ake na ganin an kauce wa barkewar yakin duniya na uku, wanda ake ganin cewa yaki ne na makamin kare dangi, wanda Koriya ita ma ta mallake shi, kuma ita ce ake ganin za ta iya rufe ido ta kai wa kasashen Yamma, da nufin a yi ta ta kare.

Trump da Kim sun gaisa yayin da suka dauki hotuna a gaban wasu tutocin Amurka da na Koriya ta Arewa.

Daga nan kuma suka dan taka inda suka yi wa manema labarai jawabai.

“A gaskiya mun sha gwagwagwa kafin mu kai ga samun nasarar yin wannan ganawa da juna. Amma dukkan mu muna da yakinin cewa za mu samu nasarar abin da muka sa a gaba.”Inji Kim.

Ya kara da cewa amma dai mun shawo kan kiki-kakar da ta nemi kawo cikas, tunda gas hi har mun gana.

Daga nan kuma suka kara yin musabaha da juna, har tsawon sakan 10, sannan suka ce za su ci gaba da ganawa.

Su kadai ne za su gaba a kebance, sai kuma masu yi musu tafinta.

Trump dai ba ya jin yaren Koriya ta Arewa, haka shi ma Kim ba Turanci ya ke ji ba.

Gaba daya duniya dai na sa ran ganin cewa wannan ganawa za ta haifi da mai ido, musamman batun lalata makaman nukiliya na kasar Koriya ta Arewa, wanda Turai ta Yamma da Amurka ke ganin cewa babbar barazana ce gare su da kuma tattalin arzikin kasashen su da ma kutunguilar siyasar diflomasiyyar su.

Ana kuma sa ran Amurka za ta tabbatar wa Koriya ta Arewa cewa za a buda mata hanya tare da daga mata kafa wajen fadadawa da inganta tattalin arzikin ta, muddin ta lalata makaman nukiliyar ta.

An dai maida Koriya ta Arewa saniyar-ware a siyasa da tarayyar tattalin arziki na duniya. Amma wannan mashahuriyar ziyara da Kim ya kai Singapore har ya gaba da Trump, za ta iya zama mabudin bude wa kasar kofa.

Haka kuma nasarar wannan taron zai iya kawo karshen barci da ido daya da Amurka da Turai ke yi, a cikin zullumin cewa a ko yaushe Kim zai iya kyarta ashanar banka musu makaman nukiliya.

An shafe shekarar 2017 Koriya ta Arewa na gwajin makaman linzami masu cin dogon zango, wadanda za a iya dura wa nukiliya, a cilla su kai hari kasashe da dama.

Sannan kuma Kim da Trump shun sha yi wa juna barazana, hargowa da nuna yatsa a baya.

Duniya ta cika da mamakin yadda aka samu nasarar yin wannan taro, ganin cewa shugabannin biyu dukkan su ‘yan ta-kife ne, ba mai jin shawarar mashawarta, matsawar suka sa kan su yin abin da suka ga dama.

Koriya ta Kudu ce za ta fi cin moriyar wannan taron muddin ya yi nasara, kasancewa sun hada kan iyaka daya. Kuma dama a baya kasa day ace, amma aka raba ta biyu, ta Arewa ta bi tsarin Gurguzu da Makisanci.

Idan ba a manta ba, cikin watannin baya an yi wata ganawar farko tsakanin shugaban Koriya ta Arewa da shugaban Koriya ta Kudu. Sun gana a kan iyakar kasashen biyu.

Share.

game da Author