An kama wata mata dauke da kullin tabar wiwi tana kokarin shiga kurkukun Kuje

0

Kakakin rundunar masu kula da gidajen yari na Kuje dake Abuja Chukwuedo Humphrey ya bayyana cewa jami’an sa sun kama wata mata mai suna Ijeoma Joseph a daidai tana kokarin kutsawa gidan yarin dauke da daurin mandulolin tabar wiwi.

Humphrey ya ce sun kama Ijeoma dauke da wannan taba ne a lokacin da ma’aikatan su ke bincike masu kawo wa ‘yan uwan su dake daure a ziyara.

” Da muka fara bincikar kwalin da Ijeoma ke dauke da shi sai muka gano cewa an boye taban wiwi din a cikin ledar biskit da ke daure da wasu kaya a cikin kwalin.

” Daga nan ne fa ta furta mana cewa wani ne mai suna Daniel ya aiko ta da wadannan kwali domin ta kai wa dan uwansa dake daure a gidan yarin mai suna Miracle Amechi.

Humphrey ya ce tuni sun mika ta ga hukumar (NAFDAC) domin a ci gaba da yi mata bincike a kai.

Share.

game da Author